’Yan bindiga sun yi garkuwa da budurwa a Kebbi

’Yan Sanda sun tabbatar da garkuwa da wata budurwa mai shekara 18 da sanyin safiyar Juma’a a unguwar Gangaren NEPA da ke garin Birnin Kebbi, Jihar Kebbi. Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kebbi, DSP Nafi’u Abubakar ya tabbatar wa manema labarai hakan a Birnin Kebbi. Shekara 25 bayan gwajin rigakafin Pfizer a Kano, har […]

’Yan bindiga sun yi garkuwa da budurwa a Kebbi

Garkuwa da mutane

’Yan Sanda sun tabbatar da garkuwa da wata budurwa mai shekara 18 da sanyin safiyar Juma’a a unguwar Gangaren NEPA da ke garin Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kebbi, DSP Nafi’u Abubakar ya tabbatar wa manema labarai hakan a Birnin Kebbi.

Abubakar ya ce ’yan sanda na kokarin ganin an kubutar da budurwar daga lamarin da  ya ritsa da ita.

Ya kuma bukaci jama’a da su taimaka da bayanan da za su taimaka wajen samun nasarar ceto baiwar Allar.

Rundunar ta kuma roki jama’ar jihar da su kai wa jami’an tsaro rahoton duk wata alama da ke da alaka da barazanar tsaro don daukar matakin da ya dace.