’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe

Wanda aka yi garkuwan ya taso ne daga Makurdi sansaninsa, domin halartar jana’izar ɗan uwansa da ya rasu a lokacin da aka ɗauke shi zuwa wani wuri

’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani jami’in Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) Nathaniel Terwanger Kumashe a ƙauyensa da ke ƙaramar hukumar Tarka a Jihar Benuwe.

An samu rahoton cewa wanda aka yi garkuwan ya taso ne daga Makurdi sansaninsa, domin halartar jana’izar ɗan uwansa da ya rasu a lokacin da aka ɗauke shi zuwa wani wuri da ba a san inda yake ba.

Wani kawun wanda aka yi garkuwan, tsohon mai baiwa gwamnan Jihar Benuwe shawara kan harkokin sufuri, Cif Yimam Aboh, ya shaidawa manema labarai a Makurdi ta wayar tarho cewa an ɗauke jami’in, Insfekta Kumashe a daren Laraba da misalin ƙarfe 10 na dare.

Ya ce, ’yan bindigar sun yi ta harbi don tsoratar da ’yan uwa da maƙwabta kafin su yi awon gaba da wanda suka yi garkuwan daga gidansu da ke Tse Aboh, Uchi-Mbakor a ƙaramar hukumar Tarka.

Ya kuma bayyana cewa, Kumashe ya koma gidansa ne bayan rasuwar ɗan uwansa wanda za a yi jana’izarsa a yau lokacin da masu garkuwar suka farwa gidan.

A halin da ake ciki, jami’ar hulɗa da jama’a ta Hukumar FRSC a Benuwe, Ngozi Ahula, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ƙara da cewa an kai rahoton lamarin ga ’yan sanda.