’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:15 na dare, inda maharan su uku riƙe da bindigogi da adduna suka rufar wa gidan.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani matashi mai shekaru 20, Muhammed Bello a ƙauyen Zakirai da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa ta Jihar Kano.
Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da ’yan bindigar suka kai hari a gidan wani mai suna Alhaji Yusha’u Ma’aruf, wanda yake da wani asibiti mai zaman kansa a ƙauyen na Zakirai.
Kazalika, wani ɗan gidan mai suna Abubakar Yusha’u mai shekaru 23 ya samu rauni yayin da ’yan bindigar suka guntule masa yatsa ɗaya a hannunsa na hagu.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:15 na dare, inda maharan su uku riƙe da bindigogi da adduna suka rufar wa gidan Alhaji Yusha’u.
Kazalika, maharan sun arce da wayoyin hannu da kuɗaɗe da ba a kai ga tantance ko nawa ba ne.
Kakakin rundunar ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin da bincike ya soma gudana a kansa.
SP Kiyawa ya ce tuni ’yan sanda suka fara farautar ɓata-garin domin ceto matashin da aka yi garkuwa da shi.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne ’yan sanda suka kama wasu mutum huɗu da ake zargin ’yan bindiga ne, sannan ta ƙwace makamai da alburusai da kuɗi kimanin naira 1,028,800 a unguwar Hotoro da ke Jihar Kanon.