’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 20 a Neja

Mahara sun yi garkuwa da mutum 20 a wani kauye a Karamar Hukumar Shiroror ta Jihar Neja. ’Yan bindidar sun far wa kauyen Adagi ne da safiyar Alhamis, amma babu labarin ko akwai wanda suka kashe a harin. Sun kai mamaya a kauyen ne jim kadan bayan wasu mahara sun kai hari a garin Kagara […]

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 20 a Neja

Mahara sun yi garkuwa da mutum 20 a wani kauye a Karamar Hukumar Shiroror ta Jihar Neja.

’Yan bindidar sun far wa kauyen Adagi ne da safiyar Alhamis, amma babu labarin ko akwai wanda suka kashe a harin.

Sun kai mamaya a kauyen ne jim kadan bayan wasu mahara sun kai hari a garin Kagara da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar.

Majiyarmu ta ce maharar sun kai farmaki ne a kan babura inda suka yi ta harbi a iska.

Hakan ta sa mazauna ranta a na kare domin tsira da rayuwarsa ko kuma fadawa yin garkuwar da su.

Wakilinmu bai samu jin ta bakin ‘yan sanda ba zuwa lokacin wallafa wannan labarin.