‘Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban NBA a Edo

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriyar wato NBA reshen Auchi A.O. Itemuagbo tare da kashe uwargidansa. An yi garkuwa Itemuagbo a Ehor, a hanyar Benin zuwa Auchi dake karamar hukumar Uhunmwode a jihar. Rahotanni na  bayyana cewa, an kashe uwargidan tsohon […]

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban NBA a Edo

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da tsohon shugaban kungiyar lauyoyin Najeriyar wato NBA reshen Auchi A.O. Itemuagbo tare da kashe uwargidansa.

An yi garkuwa Itemuagbo a Ehor, a hanyar Benin zuwa Auchi dake karamar hukumar Uhunmwode a jihar.

Rahotanni na  bayyana cewa, an kashe uwargidan tsohon shugaban da kuma dauke gawar zuwa wani wuri daban.