’Yan bindiga sun yi wa dagaci yankan rago a Kaduna

Kansilan Dandamisa, Alhaji Aminu Sani Marke, ya ce an gaza gano gawar dagacin saboda gidan ya ƙone ƙurmus.

’Yan bindiga sun yi wa dagaci yankan rago a Kaduna

Wasu ’yan bindiga sun kashe Dagacin garin Marke da ke Unguwar Dandamisa ta Ƙaramar Hukumar Makarfi a Jihar Kaduna, Malam Kabiru Mohammed.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na daren ranar Alhamis yayin da ’yan bindigar da ake zargin turo su aka yi suka yi wa gidan dagacin ƙawanya.

Bayanai sun ce ’yan bindigar da su riƙa lalube sun gano dagacin wanda ya ɓuya a cikin rufin kwanon gidansa tare da wani yayansa, Tukur Mohammed.

A cewar wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ’yan bindigar bayan sun gano dagacin sun yi masa yankan rago sannan suka cinna wa gidan wuta.

Da yake martani kan lamarin, Kansilan Unguwar Dandamisa, Alhaji Aminu Sani Marke wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an gaza gano gawar dagacin saboda gidan ya ƙone ƙurmus.

Wani sashe na gidan dagacin da ’yan bindigar suka ƙone

Ya ce, “’yan bindigar sun shafe kusan awa ɗaya suna sheƙe ayarsu a ƙauyen sannan suka yi awon gaba da dukiya ta miliyoyin naira.”

Marigayi Kabiru Muhammad, mai shekaru 30, an naɗa shi a Dagacin garin Marke a shekarar 2018.

Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna kan lamarin amma ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.