’Yan bindiga sun yi wa masu taron Mauludi yankan rago a Katsina

’Yan bindiga sun kashe mutane 25 sun jikkata wasu a taron Mauludi a Karamar Hukumar Musawa ta Jihar Katsina

’Yan bindiga sun yi wa masu taron Mauludi yankan rago a Katsina

wuka

’Yan bindiga sun yi wa mutane yankan rago a wani taron Mauludi a yankin Kusa da ke Karamar Hukumar Musawa a Jihar Katsina.

’Yan bindigar sun kashe mutumu 25, baya ga wasu 17 da suka tsallake rijiya da baya da aka kwantar a Babban Asibinin Musawa da kuma Asibitin Koyarwa na Katsina, a sakamkon raunukan da suka samu a harin.

Aminiya ta gano mahalartar Mauludin sun zo taron ne daga kauyuka daban-daban na kanana hukumomin Musawa da kuma Matazu.

Daya daga cikinsu da aka kai Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina ya ce, ’yan bindigar , “Zagaye mu suka yi suka fara harbi, da mutane suka fara guduwa sai suka fara harbin wasu, wasu kuma suka yi musu yankan rago.

“Sun harbe ni a gwiwa sannan suka sare ni da adda a hannu suna cewa wannan alama ce ga duk wadanda suka kwakkwanta kamar sun mutu.”

Mahaifin daya daga cikin wadanda abin ya shafa, Malam Salisu, ya ce sun fara jin harbe-harbe ne da misalin karfe 10:30 na dare a lokacin da yaran ke wurin taron Mauludin, inda aka kashe muum 23, wasu 16 suka jikkata, ciki har da dansa mai shekaru tara.

“Mun kawo mutum 16 da suka samu rauni asibiti, amma biyu daga cikinsu sun rasu kafin mu karaso; mutum 25 ke nan suka rasu,” in ji shi.

Ya bayyana cewa kafin jami’an tsaro su kawo dauki, maharan sun riga sun tsere.

Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina ya ziyarci yankin inda ya jajanta wa al’ummomin ya kuma jaddada aniyarsa ta ganin an samu tsaro a jihar.

A yayin ziyarar ta’aziyya da dubiyar da ya je, dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Musawa da Matazu, Abdullahi Aliyu Ahmed, ya ce sama da mutum 20 ne suka bace bayan harin.

Da yake tabbatar da harin, kakakin ’yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce nan take ’yan bindigar suka kashe mutum bakwai, suka jikkata wasu 18 da aka garzaya da su asibitin Musawa.

“Wasu mutum biyu sun mutu daga baya. Muna bincike domin kama wadanda suka yi wannan aika-aika, don ganin sun fuskanci hukunci,” in ji jami’in.