‘Yan bindiga sun yi yunkurin halaka Dokta Datti Ahmad a Kano
Shugaban Majalisar koli ta Harkokin Shari’ar Musulunci (SCSN) Dokta Ibrahim Datti Ahmad, ya tsallake rijiya da baya bayan da wasu ’yan bindiga hudu suka kai masa hari a gidansa da jijjifin shekaranjiya Laraba.Aminiya ta samu labari daga wadanda lamarin ya faru kan idonsu cewa ’yan bindigar dauke da kananan bidigogi sun daure masu gadin malamin […]

Shugaban Majalisar koli ta Harkokin Shari’ar Musulunci (SCSN) Dokta Ibrahim Datti Ahmad, ya tsallake rijiya da baya bayan da wasu ’yan bindiga hudu suka kai masa hari a gidansa da jijjifin shekaranjiya Laraba.
Aminiya ta samu labari daga wadanda lamarin ya faru kan idonsu cewa ’yan bindigar dauke da kananan bidigogi sun daure masu gadin malamin su biyu bayan sun tsallaka zuwa cikin gidansa da ke Titin ’Yandutse a Unguwar Nasarawa da ke kusa da Gidan Gwamnatin Jihar Kano ta saman katanga.
Lamarin wanda karfe 2:00 na dare wayewar Laraba, an ce maharan sun fada cikin gidan Dokta Datti inda suka fasa wata taga lokacin da suka suka kasa shiga ta kofa bayan sun yi ta bugawa a bude musu ba a bude ba.
Dokta Datti wanda ya tabbatar wa wakilanmu da faruwar lamarin ya ce, bai san dalilin kai masa harin ba, kuma ya ce ya sanar da hukumomin tsaro wadanda ya ce su ne za su iya gano hakikanin dalilin kai masa wannan hari.
Ya ce maharan suna kokarin tsorata shi ne, kuma zai ci gaba da addu’a, inda ya ce bai kaurace wa gidan ba bayan aukuwar lamarin.
daya daga cikin masu gadin gidan Dokta Datti ya bayyana cewa ’yan bindigar wadanda ko rufe fuskokinsu bas u zyi ba, sun fada gidan ne a lokacin da suke barci, inda suka umarce su kan su nuna musu dakin malamin.”Lokacin da muka shaida musu cewa ba mu san inda maigidanmu yake ba, sai suka daure mu da igiya, suka dora bindiga a kanmu suna barazanar za su kashe mu idan muka yi yunkurin ihu,” inji shi.
Ya ce “ Daga nan sai suka nufi cikin gidan suka fara kwankwasa kofa. Da suka ji shiru, sai suka yi amfani da bindiga suka fara wata taga wadda suka shiga wani daki ta cikinta. Amma bayan wasu mintoci suna neman maigidanmu ba su samu ba, sai maharan suka yanke shawarar barin gidan, suna rantsuwa cewa za su dawo su kashe maigidanmu.”
Ya ce jim kadan da tafiyar maharan ne sai wani rukunin ’yan sanda ya iso gidan cikin motoci hudu suna harbin iska don nuna sun iso. “’Yan sanda ne suka zo suka kwance mu sannan suka zauna a gidan har zuwa wayewar gari kafin su tafi,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya musanta cewa haring a Dokta Datti hari ne na yunkurin halaka shi, inda ya dora laifin hakan kan ’yan fashi da makami.
Ya ce “Ba yunkurin kisan gilla ba ne. Wasu ’yan fashi da makami ne suka kai hari gidan Dokta Datti, amma suka kasa shiga gidan saboda ’yan sanda sun kai dauki cikin gaggawa.” Kuma ya ce, a lokacin harin ba wanda aka yi wa rauni ko aka halaka.
Dokta Datti wanda malamin addini ne kuma likita ya yi kokarin shiga don sasanta tsakanin ’yan kungiyar Boko Haram da Gwamnatin Tarayya, amma daga baya ya janye yana zargin rashin gaskiya daga bangaren gwamnati bayan da aka fallasa bayanan tattaunawar ga kafafen watsa labarai a bara.
Har wa yau Gwamnatin Tarayya ta sanya sunan Dokta Datti a cikin Kwamitin Shugaban kasa don Tattaunawa da Waware Rikicin da ke Addabara Arewa a karkashin Minista Ayyuka na Musamman Kabiru Turaki wanda aka dora wa alhakin tattaunawa da kungiyar Boko Haram, amma Dokta Datti da Shehu Sani wani dan kare hakkin dan Adam da ke Kaduna suka ki shiga kwamitin.
Yayin da Dokta Datti ya soki kwamitin cewa zai goyi bayan gwamnati ne kawai, Sani a banagrensa ya ki shiga kwamitin ne kan cewa ba a tuntube shi ba kafin a sanya shi a ciki.