’Yan bindigar da suka sace almajirai a a Sakkwato sun buƙaci fansar N20m
’Yan bindigar da suka sace ɗaliban sun kira malaminsu ta wayar salula.
‘Yan bindigar da suka sace almajirai 15 a Jihar Sakkwato sun bukaci a biya su kuɗin fansa har naira miliyan 20 kafin su sako su.
Alaramman Tsangayar, Liman Abubakar ne ya bayyana haka ga wakilinmu a ranar Talata.
Ya ce, “’yan bindigar sun kira ni sau biyu yau da safe.
“A waya ta farko, sun tambaye ni ko ban damu da halin da ɗalibaina suke ciki ba shi ya sa ban tuntube su ba?
“Sai na ce musu ba ni da lambarsu shi ya sa. Sai su ka ce, in jira za su sake kira da misalin ƙarfe 11 na safe.
- Hatsaniya Ta Barke A Majalisar Dattawa Kan Kuɗin Rabon Tallafi
- SSANU da NASU za su shiga yajin aikin gargadi
“Bayan karfe 11 na safe, sai suka sake kira, suka umarce ni da in je in zauna da Hakiminmu, in faɗa masa cewa ya nemo Naira miliyan 20, domin su sake su.
“Na roke su amma sun ce ba za su rage komai ba. Na je na tattauna batun da hakimin ƙauyenma amma har yanzu ba mu cimma matsaya ba.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Asabar da ta gabata ce ’yan bindiga suka sace ɗaliban Tsangayar da ke Gidan Bakuso a Karamar Hukumar Gada ta Jihar Sakkwato.
Bayanai sun ce an ɗauke ɗaliban ne a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa zuwa dakunansu domin gujewa harin da ‘yan bindigar suka kai wa al’ummar yankin.