‘’Yan bindigar da suka tsare mu sun raba mana aiki’
Ba ma samun matsala da su idan lokacin sallah ya yi.
Daya daga cikin fasinjojin da suka kubuta bayan an yi garkuwa da su a jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna a watan Maris, Hassan Aliyu, ya bayyana yadda suka yi rayuwa a cikin daji.
A tattaunawarsa da Aminiya, Aliyu ya ce kwana 70 da suka yi a hannun ’yan bindiga shi da ‘yan uwansa ana ciyar da su da shinkafa da tuwo da aka girka a mummunan yanayi.
Ya bayyana cewa, wasu daga cikin matan da aka yi garkuwa da su na girki da wanke-wanke yayin da maza ke zuwa debo ruwa da kawo itacen girki.
“Muna cin abincin ne kawai don mu rayu, amma akwai yawa. Suna ba mu wadataccen abinci.
“Muna girka shinkafa da manja da magi, kuma har sauyin abincin muke samu da tuwon masara,” in ji shi.
Aliyu ya kara da cewa, ba su da matsala kan yin Sallah, don ba a taba hana su yi ba ta kowace hanya. Sai dai kawai ba su da ’yanci duk inda za su sai da izini.
“Duk abin da za ka yi sai ka nemi izini. Lokaci daya da ba za ka nemi izini ba shi ne idan za ka tattauna da abokan zamanka.
“Ba a batun sauyin tufafi saboda kowa daya yake sanyawa, suna ba mu omon wanki da sabulun wanka. Sai mu je kudiddifi mu yi wanka, mu wanke tufafinmu mu jira su bushe mu dawo,” in ji shi.
Idan an fara ruwan sama, Aliyu ya ce akwai wasu runfunan kwano uku zuwa hudu.
“Sai duk mu shiga ciki mata su dauki daya, daga bisani suka gina babba. Idan ruwan ya yi yawa sai mu kwana a ciki.”