’Yan bindigar Katsina ku rungumi sulhu

Ina son yin amfani da wannan dama don yin kira ga masu kai hare-hare a kauyukan Jihar Katsina cewa su yi wa Allah sun rungumi shirin sulhu da gwamnatin jihar take kokarin yi da su. Su daina kai hare-hare ga jama’a suna kashe mutane ba su ji ba, ba su gani ba tare da kwashe […]

’Yan bindigar Katsina ku rungumi sulhu
’Yan bindigar Katsina ku rungumi sulhu

Ina son yin amfani da wannan dama don yin kira ga masu kai hare-hare a kauyukan Jihar Katsina cewa su yi wa Allah sun rungumi shirin sulhu da gwamnatin jihar take kokarin yi da su. Su daina kai hare-hare ga jama’a suna kashe mutane ba su ji ba, ba su gani ba tare da kwashe musu dabbobi da kuma raba su da muhallansu.

Tun bayan bikin Babbar Sallah hare-hare suka kara yawaita musamman a kauyukan da suke kananan hukumomin Kankara da Danmusa da Safana da Batsari da kuma Jibiya. Hare-haren sun hallaka rayukan jama’a da dama sannan sun sanya mata da kananan yara suna galaibaita yayin da dukkan al’ummomin yankin suka fada cikin mawuyacin hali. Kuma maharan kuna talauta ’yan uwansu da sanya kunci da tilasta musu yin gudun hijira. Ya kamata ku tuna cewa zama lafiya shi ne kan gaba a rayuwar duk wani mutum ko al’umma, don haka ko dabbobi da kudin da kuke karba a hannun mutane ba za su ciwu ta dadi ba tunda ku kanku kuna zaman kunci da buya ne.

Ya dace ku natsu ku gane cewa masu kawo muku makamai kuna saye mutane ne da suke amfani da wannan tashin hankali don azurta kansu kawai. Ba za su taba yarda koda wasa ba su zo su shiga cikinku a kai hari tare da su. Yayin da kuke sanya kanku a hadari na zaman jira ko ku kashe ko a kashe, su kuwa suna can su da ’ya’yansu suna shan raba suna zaune a gidajensu lafiya da makwabtansu. Yayin da kuke ta faman sace dabbobin abokan zamanku su kuma suna can suna amfani da kudin da suka karba daga wajenku suna gina nasu garuruwa tare da tallafa wa nasu abokan zaman. Kuna lalata jiharku su kuma suna kara gyara tasu da guminku da na makwabtanku.

Don haka ya kamata ku yi wa Allah ku rungumi shirin sulhu da Gwamna Aminu Masari ya bullo da shi don a zauna da ku a tattauna a samu mafita kamar yadda ya wakana a a Jihar Zamfara. Haka zai sanya ku kanku ku samu salama da dawowa a ci gaba da zama da makwabta lafiya. Ya kamata ku daina dari-dari da wannan shiri saboda umarnin da Shugaban Kasa ya ba soja na hallaka duk wani dan bindiga ba zai shafi wanda ya fito fili ya ya tuba kuma ya bayyana nadamarsa da kuma niyyarsa ta zaunawa lafiya da kowa ba.

 

Iro Surajo, Abuja (0816 343 9197)