’Yan bingida sun sace mutane 40 a coci a Kaduna
Gwamnatin Kaduna da rundunar ’yan sandan jihar ba su ce komai ba har yanzu dangane da harin.
Wasu ’yan bindiga sun sace mutane 40 a yayin da ake tsaka da ibada a Cocin Bege da ke a garin Madala a Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) Reshen Jihar Kaduna, Rabaran John Joseph Hayab ya ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 9:30 na safe.
A sanarwar da ya fitar, Rabaran Hayab ya bayyana cewa ’yan bindigar sun rika yin harbi domin tsorata mutane a “cocin sannan suka yi awon gaba da mutanen su 40.”
Sai dai ya bayyana cewa akalla mutum goma sha biyar daga cikin wadanda aka sacen sun samu tserewa, amma akwai sauran mutum 25 a hannun ’yan bindigar.
Ya kara da cewa suna kokarin wajen ganin an zanta da ’yan bindigar domin a san yadda za a karbo mutanen da ke hannunsu.
Wasu daga cikin mutanen da suka kubuta sun bayyana cewa harin ya matukar tsorata su domin ’yan bindigan sun zo wajen ne da yawansu rike da makamai.
Gwamnatin Jihar Kaduna da rundunar ’yan sandan jihar ba su ce komai ba har yanzu dangane da harin.