’Yan Biyafara sun kashe shugabannin al’umma 8 a Imo

Maharan sun kai harin ne yayin da shugabannin suke tsaka da gudanar da taro.

’Yan Biyafara sun kashe shugabannin al’umma 8 a Imo

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ta bayyana cewa wasu ’yan awaren Biyafara sun harbe wasu wasu mutane takwas a garin Umucheke da ke ƙaramar hukumar Onuimo.

Kwamishinan rundunar, Mista Aboki Danjuma, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi lokacin da ya jagoranci wasu shugabannin hukumomin tsaro zuwa wajen da harin ya faru.

Danjuma, ya ɗora alhakin harin a kan ’yan awaren Biafra.

Ya ce a halin yanzu rundunar ’yan sanda tare da haɗin guiwar rundunar sojojin Najeriya da jami’an tsaron Sibil Difens na ƙoƙarin gano waɗanda suka kai harin.

“Sun kai harin ne a kan babura guda uku; al’ummar sun ce ssun gansu amma ba su kai rahoto ga ‘yan sanda ba.

“Ya kamata mazauna Imo su kasance masu lura tare da kai rahoto ga ‘yan sanda domin daƙile hare-haren ɓata-gari,” in ji shi.

Ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu da kuma al’ummar Umucheke bisa harin.

Ya kuma ba su tabbacin cewa jami’an tsaro suna bakin ƙoƙarinsu wajen kamo waɗanda da suka harin.

Ya ƙara da cewa, rundunar ’yan sandan za ta girke jami’an tsaro a yankin domin ƙarfafa tsaro.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), ya ruwaito cewar waɗanda aka kashe sun haɗa da shugaban al’ummar yankin, Mista Hyginus Ohazurike da wasu hakimai bakwai.

An ruwaito cewa an kai musu hari ne a lokacin da suke gudanar da taro a yankin.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewar, ba a san dalilin kai harin ba.

NAN ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne mako guda bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wasu sassan Owerri, babban birnin Jihar Imo, inda suka kashe ‘yan sanda biyar da wasu mutum uku.

Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas