’Yan biyu na aiki a gidan abinci babu kakkautawa a kasar Sin

Wani gidan abinci da ke garin Yiwu a kasar sin, ana hada-hada a cikinsa babu kakkautawa, har ta kai ga masu cin abinci a wurin sun kasa gane yadda ma’auratan da suka mallaki wuri ke aiki tukuru, babu dare, babu rana. Wasu ma na gani masu gidan abincin ba su da hutu, alhali wani sirri […]

’Yan biyu na aiki a gidan abinci babu kakkautawa a kasar Sin

Wani gidan abinci da ke garin Yiwu a kasar sin, ana hada-hada a cikinsa babu kakkautawa, har ta kai ga masu cin abinci a wurin sun kasa gane yadda ma’auratan da suka mallaki wuri ke aiki tukuru, babu dare, babu rana. Wasu ma na gani masu gidan abincin ba su da hutu, alhali wani sirri ne da suka boye wa jama’a
Saboda aikin da suke a tsakanin karfe shidda na safe zuwa ukkun dare, sai aka yi musu lakabin ma’aurantan na’ura mai sarraf akanta “Robot Couple.” Daga bisani dai an gano sirrin da ke tattare da wadannan ma’aurata masu gidan abinci, inda ta bayyana cewa ’yan biyu masu kama daya, suka auro mata ’yan biyu da ke taya su aiki.
Wadannan ’yan biyu maza, shekarunsu 32, sun kuma auri mata ’yan biyu. Kuma suna yin karba-karba a wajen tafiyar da gidan abincinsu. Sannan suna da ’ya’ya biyu maza, wadanda suka yi kama da juna. Wadannan iyalaiu suna sha’awar zama tare da juna, don haka suke aiki tare wajen tafiyar da gidna abincinsu.
Iyalan na matukar jin dadin lakabin da ka yi musu na “Iyalan na’ura mai sarrafa kanta – Robot couple.”