‘Yan Boko Haram 36 sun mika wuya a Borno
Shalkwatar tsaro ta kasa ta ce akalla mayakan kungiyar Boko Haram 13 tare da iyalansu mata shida da kananan yara 17 da suka fito daga kauyen Koidila ne suka mika wuya ga rundunar a jihar Borno. ‘Yan ta’addan dai sun mika wuyan ga bataliyar runduna ta 151 dake kusa da garin Banki a karamar hukumar […]
Mayakan Boko Haram
Shalkwatar tsaro ta kasa ta ce akalla mayakan kungiyar Boko Haram 13 tare da iyalansu mata shida da kananan yara 17 da suka fito daga kauyen Koidila ne suka mika wuya ga rundunar a jihar Borno.
‘Yan ta’addan dai sun mika wuyan ga bataliyar runduna ta 151 dake kusa da garin Banki a karamar hukumar Bama ta jihar.
- Boko Haram: Akwai ayar tambaya tsakanin gwamnati da sojoji – Dattawan arewa
- Sojoji sun karkashe kwamandojin Boko Haram
Shugaban cibiyar da ke samar da bayanai kan ayyukan rundunar John Enenche shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a Abuja ranar Lahadi.
Ya ce ‘yan ta’addan sun mika wuya ne bayan hare-hare da dakarun rundunar Operation Lafiya Dole su ka kai a yankin Arewa maso Gabas.
Mista John ya ce ‘yan Boko Haram din da su da iyalan nasu na can na samun kulawa daga wani asibitin sojoji.
A cewarsa, yanzu haka ana can ana fadada bincike a kansu domin tabbatar dacewa baya ba ta haihu ba daga bisani.
Ya kara da cewa rundunar sojojin da hadin gwiwar sauran jami’an tsaron Najeriya za su ci gaba da kara kaimi wajen ganin sun kakkabe dukkan bata-gari.