’Yan Boko Haram 51,828 sun mika wuya — Irabor

Lallai sojoji sun fuskanci kalubale kala-kala a yayin fafatawa da mayakan na Boko Haram.

’Yan Boko Haram 51,828 sun mika wuya — Irabor

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor

Kimanin ’yan Boko Haram dubu 51 da 828 sun mika wuya ga dakarun sojin Najeriya a tsakanin watan Yulin 2021 zuwa Mayun 2022.

Babban Hafsan Hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor ne ya fadi haka a yayin gabatar da wata makala a Jami’ar Edo, yana mai cewa, dubu 13 da 360 daga cikin ’yan Boko Haram din mayaka ne.

Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriyar ya kuma kara da cewa, dubu 1 da 543 daga cikin tubabbun mayakan na Boko Haram sun kammala zaman gyaran hali a sansanin Mallam Sidi tsakanin 2016 zuwa 2022, yayin da dubu 1 da 935 aka sauya musu tunani a sansanin Bulumbuktu.

A cewarsa, sojojin Najeriya sun samu jerin nasarori a yakinsu da mayakan na Boko Haram, tare da kakkabe su daga maboyarsu.

Sai dai kuma Irabor ya ce, lallai rundunar Operation Safe Corridor ta fuskanci kalubale kala-kala a yayin fafatawa da mayakan na Boko Haram da suka hada da karancin kayayyaki da horo da samun goyon bayan kasa da kasa.

Dubban mutane ne suka rasa rayukansu a sanadiyar rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya, yayin da miliyoyi suka kaurace wa gidajensu.