‘Yan Boko Haram 69 sun miƙa wuya ga Rundunar MNJTF
An kuɓutar da iyalan ‘yan Boko Haram 12, da suka haɗa da mata 5 da yara 7, tare da miƙa su ga sojojin sashe na 1, Operation Haɗin Kai.
Mayakan kungiyar Boko Haram 69 da ‘yan uwansu sun miƙa wuya ga Rundunar Haɗin Gwiwa Ta Ƙasa Da Ƙasa (MNJTF) a Kamaru da Nijar da ke yankin Tafkin Chadi.
Babban jami’in yaɗa labarai na rundunar soji da ke N’djamena-Chad, Laftanar-Kanar Abdullahi Abubakar a wata sanarwa ya ce, ’yan tayar da ƙayar bayan sun miƙa wuya ne a tsakanin ranakun 1 zuwa 6 ga watan Yulin 2024, yayin da rundunar Operation Lake Sanity 2 ke ci gaba da samun nasara a kansu.
- Tinubu ya ƙirƙiro ma’aikatar harkokin kiwon dabbobi
- Yadda Aka Kashe Mayakan ISWAP 11 A Dajin Sambisa
Laftanar-Kanar Abubakar ya bayyana cewa, farmakin da sojojin Kamaru da Najeriya ke kaiwa a Tafkin Chadi, sun taimaka wajen miƙa wuyan mayaka 56 da suka haɗa da maza 13, mata 43, da ƙananan yara a ranar 6 ga watan Yulin 2024.
Hakazalika, an kuɓutar da iyalan yyan Boko Haram 12, da suka haɗa da mata 5 da yara 7, tare da miƙa su ga sojojin sashe na 1, Operation Haɗin Kai.
A wani lamari na daban kuma, wani dan kungiyar mai suna Tijjani Muhammad mai shekara 24, ya miƙa kansa da makamai da harsashi ga sojojin Jamhuriyar Nijar, a ranar 1 ga Yuli, 2024.
An bayyana cewa ya tsere ne daga sansanin Boko Haram da ke garin Libye Soroa saboda harin da sojoji ke kaiwa.
Mai sharhin nan kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi mai suna Zagazola Makama ya bayyana cewar, yunƙurin miƙa wuya yana matuƙar raunana ƙarfin ayyukan Boko Haram da mayaƙanta.
Rundunar ta MNJTF ta buƙaci sauran ’yan tada ƙaya bayan da su miƙa wuya su rungumi zaman lafiya a yankin tafkin Chadi.