’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojoji a Borno
Maharan dai sun miƙa wuya sun amsa cewa suna da hannu a ayyukan ta’addanci da dama a Arewacin Borno, inda suka nuna gajiyawa da rikicin.

Wasu ‘yan tada ƙayar baya bakwai da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun miƙa wuya ga rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) a Damasak da ke Jihar Borno tare da miƘa tarin makamai da kayan aiki.
Kamar yadda Zagàzola Makama ya ambata wannan miƙa wuyan da waɗannan maharan suka yi ga sojojin da ke aiki ƙarƙashin sashe na 3 Monguno, na nuni da nasarar da aka samu wajen yaƙi da ta’addanci a yankin tafkin Chadi.
‘Yan Boko Haram ɗin da suka miƙa wuya sun haɗa da Malam Baba Ibrahim ɗan shekara 19, Malam Bamai Ali mai shekara 20, Malam Jundu Ali mai shekara 19, Malam Abba Ali mai shekara 25, Malam Abubakar Mohammed mai shekara 20, Tijjani Ali mai shekara 20, da Malam Ali Mommudu mai shekara 25, waɗanda suka miƙa wuya bisa radin kansu ga dakarun haɗin gwiwar MNJTF a ƙauyen Walada da ke Damasak, bayan sun ci gaba da kai farmakin.
“Wannan miƙa wuya wata shaida ce da ke nuna tasirin ayyukan da muke yi a yanzu,” in ji Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, babban jami’in yaɗa labarai na soji da ke hedikwatar rundunar MNJTF.
“Waɗannan mutane sun gane rashin amfanin yaƙinsu kuma sun zaɓi hanyar zaman lafiya.”
Maharan dai sun miƙa wuya sun amsa cewa suna da hannu a ayyukan ta’addanci da dama a Arewacin Borno, inda suka nuna gajiyawa da rikicin.
Sun ce a baya suna tsoron za a kashe su idan sun miƘa wuya ga jami’an tsaron, amma a yanzu sai suka ga ba haka lamarin yake ba.
Makaman da suka miƙa ga rundunar tsaron sun haɗa da bututun makamin RPG guda biyu, bama-baman RPG guda huɗu, bindiga ƙirar AK-47, bindiga ƙirar HK 21 ta Jamus.
Har ila yau, sun miƙa dawakai guda biyu, harsasai 30 da harsasai na musamman nau’in 7.62mm, harsashi nau’in 715 na 7.62mm da wayoyin hannu 12, ƙananan na’urori masu amfani da hasken rana guda shida da wuƙaƙe guda huɗu da sauransu.
Laftanar Kanar Osoba ya ce, “Yawan adadin makamai da kayan aikin da suka miƙa ya nuna girman ayyukansu.” “Ba shakka miƙa wuyan nasu zai kawo cikas ga ayyukan ta’addanci a yankin.”
Wadannan tsoffin ‘yan tada ƙayar baya yanzu haka suna bayar da bayanan sirri ga rundunar ta MNJTF, wanda ake sa ran zai taimaka a ci gaba da gudanar da ayyukanta na yaƙi da ‘yan ta’addan a yankin tafkin Chadi.