’Yan Boko Haram 82 sun kashe juna a rikicin ƙabilanci
Mayakan Boko Haram 82 sun mutu a wani rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a tsakaninsu a yankin Kulawa da ke Jihar Borno.
Mayakan Boko Haram 82 sun mutu a wani rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a tsakaninsu a yankin Kukawa da ke Jihar Borno.
Majiyoyin tsaro da mazauna yankin Baga da ke kusa da Tafkin Chadi sun ce rikicin ƙabilancin ya kunno kai ne bayan ƙungiyar ta harbe wasu mayakanta bakwai ’yan ƙabilar Buduma, har lahira.
- Wadda ta maye gurbin Maryam Shetty ta zama Ƙaramar Ministar Abuja
- NAJERIYA A YAU: Yadda hauhawar farashi ke hana ’yan Najeriya cin abinci
Majiyarmu ta ce “Sun yi musayar wuta inda aka kashe mayaƙa 82… Amma dai rikicin na kabilanci ne.”
Ta ce kwamandan ƙungiyar ne ya yanke wa mayaƙan hukuncin harbewa bayan gano shirinsu na miƙa wuya ga sojojin Najeriya.
“Kafin su kai ga miƙa wuya ne wasu abokansu da suka ba wa labari suka sanar da kwamandan, ya sa aka daƙile su aka kai su Tsibirin Bukkwaram aka harbe su har lahira.
“Wannan ya haifar da rikici tsakanin mayaƙa ’yan ƙabliun Kanuri, Buduma, Fulani da kuma Hausawa da ke kungiyar.
“Kisan ya fusata ’yan uwansu ’yan ƙabilar Buduma, inda suke zargin kwamandan da kama-karya, ganin yadda a baya-bayan nan suke ta rasa mayaƙansu,” in ji majiyar tamu.
Ta ce bayan nan ne ƙungiyar ta kira wani zama inda kwamandojinta suka yi ittifaƙi cewa duk wanda ke buƙatar tafiya ya tafi inda ya ga dama.
“Amma ɗayansu, Baduma Bakura, ɗan ƙabikarBuduma da ya zo taron daga yankin Ali Mandula da ke Nijar ya ƙi amincewa.
“Ya ce shi ya zo ne domin ya binciki dalilin kashe ’yan ƙabilarsa, ya kuma yi barazanar harbw duk wanda ya nemi tashi daga wurin.
“Hakan ya haifar da zazzafar muhawara, ana cikin haka kuma wani bafulatani ya harbe shi har lahira.
“Mayaƙa 82 aka kashe kuma ba za a iya ware ’yan Boko Haram ko ’yan ISWAP a cikinsu ba. Amma dai rikicin na kabilanci ne,” in ji wata majiyar tsaro.
Majiyar ta ce daga cikin mayaƙan aka kashe a rikicin akwai sanannun fuskokin ’yan Boko Haram da a baya suka tsere daga yankunan Baga, Doron Baga da Kukawa zuwa Jamhuriyyar Nijar da ma yankin Sahel.
“A baya sun tsere zuwa tsallaken Tafkin Chadi amma daga baya suka dawo gida kafin rikicin ƙabilancin ya yi ajalinsu,” in ji majiyar.