‘Yan Boko Haram da ISWAP 47 sun miƙa wuya a Borno

Waɗanda suka miƙa wuyan sun haɗa da maza bakwai, mata tara da yara 31.

‘Yan Boko Haram da ISWAP 47 sun miƙa wuya a Borno

Dakarun MNJTF

Aƙalla mutum 47 da ke da alaƙa da ƙungiyoyin tayar da ƙayar-baya na Boko Haram da ISWAP sun miƙa wuya ga rundunar sojojin Amphibious Brigade ta haɗin gwiwa da ke yaƙi da ’yan ta’adda a gabar Tafkin Chadi.

Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi, babban jami’in yaɗa labarai na rundunar soji na N`djamena da Chadi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Alhamis a Maiduguri.

Abdullahi ya ce, waɗanda suka miƙa wuyan sun haɗa da maza bakwai, mata tara da yara 31.

Ya ce, iyalan ‘yan ta’addan sun koma yankin Kwatan Turare da Doron Baga, a ƙaramar hukumar Kukawa ta Jihar Borno bayan shafe shekaru da dama suna tare da ‘yan tada ƙayar bayan.

Ya bayyana cewa, a binciken farko da aka gudanar, an gano cewa waɗanda suka miƙa wuya sun yi nasarar tserewa daga Sharama, da ke cikin tsibiran Tafkin Chadi.

A cewarsa, daga cikin waɗanda suka miƙa wuya har da Malam Muazu Adamu, wanda sanannen mayaƙi ne a cikin Ƙungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad (JAS).

“Ya yi aiki a karkashin kwamanda Alai Gana kuma ya miƙa wuya tare da matarsa,” in ji shi.

Abdullahi ya ce sauran ‘yan kungiyar sun bayyana cewa sun sha yin noma kafin su yanke shawarar tserewa.

A cewarsa, kayayyakin da aka samu a hannunsu sun hada da tufafi, barguna, tabarmi, tukwane, faranti, da sauran kayayyaki na kashin kansu.