’Yan Boko Haram din da sun bambanta da na yanzu – Sheikh Diyar

Sheikh Abubakar Diyar Limamin Salafawa a garin Damaturu na daya daga cikin malaman Musulunci da aka ambaci sunansu don shiga tsakanin gwamnati da ’ya’yan kungiyar Boko Haram a sasanta, kusan shekara biyu da suka gabata, amma shirin ya sha ruwa.  A tattaunawar da wakilinmu ya yi da malamin, ya bayyana cewa da ma can shirin […]

’Yan Boko Haram din da sun bambanta da na yanzu – Sheikh Diyar

Sheikh Abubakar Diyar Limamin Salafawa a garin Damaturu na daya daga cikin malaman Musulunci da aka ambaci sunansu don shiga tsakanin gwamnati da ’ya’yan kungiyar Boko Haram a sasanta, kusan shekara biyu da suka gabata, amma shirin ya sha ruwa.  A tattaunawar da wakilinmu ya yi da malamin, ya bayyana cewa da ma can shirin ba da gaske ba ne, kuma ya ce ’yan Boko Haram din da sun sha bamban da ’yan Boko Haram na yanzu. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Akramakallah, a baya ka yi kokarin ba da gudummawarka tare da Sheikh dahiru Bauchi don a yi sulhu tsakanin ’yan kungiyar Boko Haram da Gwamnatin Tarayya, duk da hakan bai yiwu ba, a yanzu wane kudiri kake da shi dangane da wannan lamari?
Sheikh Diyar: A gaskiya kowane dan Najeriya zai so ya ba da gudunmawarsa ga ci gaban Najeriya kususun don samun zaman lafiya. Kuma hakika yadda wannan abu yake a baya a gaskiya a yanzu ba haka yake ba domin lokacin da muka so mu taimaka abubuwa ba su kai ga tabarbarewa ba kamar yadda suke a yanzu, kuma a lokacin mutanen da ke aikata wadannan abubuwa a yanzu yawancinsu sun mutu wasu kuma sun bar kasar nan, illa kalilan daga cikinsu da suke tare da ’yan Boko Haram na yanzu. Kuma a  yanzu in an ce za a nemi kawo karshen wannan dambarwa, to, lallai sai an yi jan ido domin kuwa a halin da ake ciki ya kai ga ’yan tada kayar bayan da ake da su a yanzu sun kai ga nasarar fatattakar jami’an tsaron Najeriya tare da kama garuruwa a wasu yankuna da wannan fitina ta fi tsamari, har suna  tutiyar kafa daularsu. To ka ga ashe akwai aiki tukuru kafin a samo bakin zaren wannan dambarwa, to amma kowane lokaci zaman lafiya kan iya samuwa matukar an sa kishin kasa.
Aminiya: Ka ce ko da za a kai ga samun bakin zaren shawo kan wannan lamari sai an yi jan ido, me ya sa ka fadi haka?
Sheikh Diyar: Abin da ya sa na fadi haka, shi ne a gaskiya akwai hannayen mutane da yawa cikin wannan lamari. Abu na farko kuma shi ne mafi yawan wadanda aka danka musu amanar al’umma sun gaza tafiyar da ita da gaskiya, son rai ya rinjayi amanar tasu, akwai maciya amana da yawa ta yadda ba su damu da halin da al’ummarsu ke ciki ba. Abu na gaba kuma shi ne akwai hannun dillalan makamai da suke amfana da wannan rikici, saboda shigowa da makamai da zimmar tara dukiya da kokarin tarwatsa kasa. Kana akwai hannayen wasu jami’an gwamnati. Ka ga kuwa ashe shawo kan wannan irin lamari ba karamin aiki ba ne.
Aminiya: To tunda lamarin haka yake ina mafita, kuma mene ne abin yi?
Sheikh Diyar: A hakikannin gaskiya babbar mafiya ko abin yi dangane da wannan lamari a bisa ga fahimtata, abu na farko shi ne nuna kishin kasa daga bangaren shugabanni da kuma su kansu bangarorin jami’an tsaron kasar nan da aka ba su amanar kula da rayuka da dukiyoyin al’ummar kasa ba tare da nuna wariyar yankim ko jinsi ko addini ba. Abu na gaba kuma shi ne wadannan kungiyoyin da ke tada kayar baya da sunan Boko Haram a san cewa ire-iren kungiyoyin ba a Najeriya ake da su kawai ba, akwai ire-irensu a kasashen Mali da Iraki da Afganistan da kuma Somaliya. Wadanda mafi yawansu ana zaman sulhu da su don sasantawa duk da cewa wadancan kasashe suna gwagwarmaya ne don siyasar neman mulki. Akwai kuma bambanci da ’yan tada kayar baya da ke kasar nan sabanin bayanin da wani jami’in gwamnati ya yi a  kwanaki cewa wai duk daya suke, wai kuma a nan kasar abubuwa ba su kai ga lalacewa ba kamar na wadancan kasashe. A gaskiya akwai jami’an tsaron da ke da kokarin yin aiki tukuru da rikon amana  a kasar nan, illa dai watakila ba a ba su damar tunkarar wannan tashin tashina ba ne. To me zai hana in gwamnati da gaske take yi ta tura su don neman maslaha? Sannan kuma ina kan maganata cewa duk wani yakin da ake yin sa a duniya a karshe dole ne sai an hau kan teburin shawarwari don sasantawa, amma ba da karfin bindiga ba. Don haka kada gwamnati a kullum ta rika gadarar cewa, sai ta hanyar amfani da karfi ne za ta biya bukatarta, musamman ganin cewa akasarin yaran nan  ’yan kasar nan ne. Ashe tunda haka ne bin hanyar sulhu shi ya fi ta hanyar samar da amintattun malaman da wadannan yara suka yarda da su, ba wai a nada kwamitin tsofaffin sojoji ba, ko lakcarori don sasanta wannan abu, wanda da kamar wuya tunda kwamitin da Gwamnatin Tarayya ta kafa a baya a karkashin Minista Turak har zuwa yau ban yi tsammani akwai wani abu da aka yi ba, kuma kullum lamarin dada tabarbarewa yake yi.
Aminiya: Malam in da za a gayyace a karo na biyu don shiga tsakani za ka amsa?
Sheikh Diyar: Ba shakka mutum na da damar amsa gayyata ko kin amsata, to amma a halin da ake ciki a yanzu matukar akwai gaskiya cikin wannan gayyata ba irin ta baya ba, me zai hana in amsa?  Ni Musulmi ne mai kaunar kasar nan tunda Manzon Allah (SAW) ya yi sulhu a Hudaibiyya da mutanen Makka.
Don haka ba zan ce ba zan taimaka ba, amma a sani, kamar yadda na fada a baya ne, akwai bambanci sosai tsakanin ’yan Boko Haram na farko da na yanzu, tunda yanzu babu irin jinsin mutanen da babu cikinsu, akwai masu kishin Musulunci a ciki, akwai ma wadanda ba Musulmi ba a ciki, kuma akwai ’yan daba a ciki, kai ma ba za a rasa tsirarun mutanen kasashen waje ba a cikinsu, abu dai ya cakude. Kuma ’yan Boko Haram na farko ba su da makamai irin yaran yanzu. kila lokacin da Turawa suka mamaye kasar Libya suka kashe shugabanta marigayi Mu’ammar Gaddafi, ta nan ne makamai suka warwatsu, kasancewar babu kwakkwarar gwamnatin da za ta hana. Shi ne wadansu daga cikin ’yan ta’adda suka same su suka watsu zuwa Mali da Tunisiya har suka shigo nan Najeriya, inda ’yan tada kayar baya suke amfani da su, kasancewarsu miyagun makamai da ake zaton sun dara na jami’an tsaronmu.