’Yan Boko Haram fiye da 900 sun mutu a hannun sojoji – Amnesty

kungiyar Kare Hakki dan Adam ta Duniya (Amnesty International) ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da bincike kan mutuwar daruruwan ’ya’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram a lokacin da suke tsare a hannu sojojin JTF masu aikin samar da tsaro.kungiyar Amnesty ta ce ta samu […]

’Yan Boko Haram fiye da 900 sun mutu a hannun sojoji – Amnesty

Laftana Janar Azubuike Ihejirika Hafsan Hafsoshin Najeriyakungiyar Kare Hakki dan Adam ta Duniya (Amnesty International) ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da bincike kan mutuwar daruruwan ’ya’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram a lokacin da suke tsare a hannu sojojin JTF masu aikin samar da tsaro.
kungiyar Amnesty ta ce ta samu sahihan bayanai daga wani babban jami’in sojan Najeriya cewa fiye da mutum 950 sun mutu a lokacin da suke tsare a hannun sojoji a watanni shida na wannan shekarar kadai.
Wata sanarwa da ta fitar a shafinta na intanet Amnesty ta ce galibin rahotannin mutuwar sun auku ne a wuraren da sojojin ke amfani da su wajen tsare mutanen da suke zargi suna da alaka ko ’ya’yan kungiyar Boko Haram ne.
“Shaidun da aka tattara sun nuna daruruwan mutane sun mutu a hannun sojoji a bana kadai. Wannan adadi ne mai yawa da ke bukatar gwamnatin Najeriya ta yi binicke a kai,” inji Lucy Freeman Mataimakiyar Daraktar kungiyar mai kula da Afirka.
Ta kara da cewa, “Wajibi ne a bankado hakikanin abubuwan da suka faru a boye a wadannan munanan wuraren tsaro, kuma a hukunta wadanda suke da hannu a keta hakkin dan Adam. Galibin wadannan mace-mace an samu rahoton sun auku ne a Barikin Soja na Giwa da ke Maiduguri a Jihar Borno da bangaren Alpha da ake kira Guantanamo da kuma Masaukin Shugaban kasa da aka fi sani da gadirum a Damaturu da ke Jihar Yobe.
Amnesty ta ce tattaunawar da ta yi da wadanda aka saki daga wadannan wuraren tsaro ya gano cewa mutane suna mutuwa kusan kullum a Giwa da Sashin Alpha sakamakon cinkoso da rashin iska ko hana su abinci ko kisan gillar da jami’an tsaron suke yi musu ko kuma saboda raunukan da suka samu aka ki yi musu jinya.
Rahoton na Amnesty ya ruwaito wani babban jami’in soja da ya nemi a sakaya sunansa yana cewa: “daruruwan mutane sun mutu a hannun sojojin kodai ta hanyar harbinsu ko cunkoso… Akwai lokutan da ake fitowa da mutane kullum a rika kashe su. Kimanin mutum biyar ko kusan haka ake kashewa kusan kullum.    
Lokacin da aka tuntubi Daraktan Labarai na Hedkwatar Sojan Najeriya Birgediya Janar Chris Olukolade kan lamarin a ranar Talatar da ta gabata, ya ce rundunar ba ta kwafin rahoton ba daga Amnesty, kuma idan suka samu rahoton za su yi nazarinsa tare da mayar da jawabi.
Sai dai Ministan Harkokin Cikin Gida Mista Abba Moro ya shaida wa gidan Rediyon BBC Landan cewa Gwamnatin Tarayya za ta gudanar da bincike kan zargin mutuwar mutanen a wuraren da ake tsare da wadanda ake zargi da aikata laifuffuka, yayin da sojoji ke fafutikar kawar da masu tada kayar bayan.
Mitsa Moro ya ce masu binciken za su hada da manyan jami’an hukumar gidan yari ta kasar nan.
Ministan ya amince cewa za a iya samun wadanda suka mutu amma a cewarsa, ba su kai daruruwa ba.