’Yan Boko Haram na ba wa mayakan Bello Turji horo a Sakkwato
Yaran Turji, ciki har da Illa Manawa da Bomi, wanda ya bayyana a matsayin ƙanin Turji, suna gudanar da wani taron horas da mayaka
Al’ummomi a gabashin Jihar Sakkwato sun bayyana damuwa bayan bullar rahotanni cewa jagoran ’yan bindigar nan, Bello Turji tare da mayakansa suna gudanar da atisayen dabarun yaƙi a wasu sassan Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato.
Sun kuma yi zargin cewa Turji ya kafa sansanonin horas da mayakansa kan sarrafa sabbin makaman zamanin da ya mallaka suna masu zargin cewa wasu daga cikin mayakan sun hada da tsoffin ’yan kungiyar Boko Haram.
Hukumomin tsaro sun ce ’yan ta’addan suna gudanar da atisayen ne a yankunan Bingabale, Bafarawa, Bargaja da Gebe, wadanda dukkansu ke cikin yankin Sakkwato ta Gabas, inda Turji ya dade yana cin karensa babu babbaka.
Kodinetan Ƙungiyar Rajin Adalci da Ci-ga da Shugabanci Nagari a Jihar Sakkwato, Basharu Altine Guyawa Isa, ya bayyana cewa Turji yana ci gaba da karfafa mayakansa tare da samar musu sabbin makamai a yankunan da ke kan iyakar jihohin Sakkwato da Zamfara.
Ya yi zargin cewa yaran Turji, ciki har da Illa Manawa da Bomi, wanda ya bayyana a matsayin ƙanin Turji, suna gudanar da wani taron horas da mayaka a yankin da ya tashi daga Bingabale Kudu zuwa Bafarawa Gabas da Bargaja, kusa da iyakar Sakkwato da Zamfara.
Basharu ya ce, kungiyar na gudanar da horon amfani da makamai da dabarun yaki ta amfani da sabbin makaman da suka samu, ciki har da wasu manyan makamai na zamani da ake zargin an yi amfani da su a arangamar baya-bayan nan da jami’an tsaro da ke aiki a yankin.
Bello Turji wanda ayyukan ta’addancinsa suka addabi jihohin Zamfara da Sakkwato da Neja, ya yi kaurin suna musamman lokacin da ya tare wata motar haya ya banka wa matafiya da ke cikinta wuta suka kone.
Ana ganin yana da mayaka da dama da aka tattaro daga sansanoni daban-daban a Jihar Zamfara, ciki har da na Zurmi, Sabon Birni, Anka da sauran al’ummomi.
A tsawon shekaru, Turji ya ki yarda da shirin sulhu da al’ummomin da abin ya shafa ke kokarin cimma domin su sake samun damar zuwa gonakinsu, makarantunsu, cibiyoyin kiwon lafiya da kasuwanni.
Gwamnati ta dade tana neman sa ruwa a jallo, inda a watan Oktoba 2024, tsohon Ministan Tsaro, Muhammad Abubakar Badaru, ya umarci sojojin Operation Fansan Yamma da su tabbatar da cafke shi da sauran fitattun shugabannin ’yan bindiga, ko da rai ko a mace.
A shekarar ce tsohon Babban Hafsan Tsaro kuma Ministan Tsaro na yanzu, Janar Chirstopher Musa, ya bayyana Turji a matsayin “mutumin matacce amma yana tafiya,” inda ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da hare-hare a kansa da mayakansa.
Duk da wadannan sanarwa da kuma hare-haren sojoji, Turji da tawagarsa sun ci gaba da kai hare-hare da aikata sauran laifuka a wasu sassan Arewa maso Yamma.
Rahotan mallakar sabbin makamai da mayaka da kuma atisayen ’yan ta’ddan da Turji ke jagoranta ya kara tsorata mazauna yankunan da ke iyakar jihohin Sakkwato da Zamfara wadanda tsawon shekaru suke fuskantar hare-hare akai-akai, garkuwa da mutane da kuma satar dabobi a yankin Sakkwato da Zamfara.
Wannan na zuwa na a daidai lokacin da Bello Turji ya fitar da wani sabon bidiyo yana tunkaho da kashe sojojin Najeriya, a yankin Isa da Sabon Birni da ke tsakanin jihohin Sakkwato da Zamfara.
Aminiya ta ruwaito cewa soja uku sun kwanta dama, wasu kimanin biyar sun jikkata bayan motar sojojin ta takan nakiya a yayin da suke kan hanyar kai wa al’ummar yankin Bargaja da ke Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato daukiy bayan ’yan bindiga sun kai musu hari da talatainin daren ranar Juma’a.
Rahotanni sun bayyana cewa an yi musayar wuta tsakanin sojoji da al’ummar yankin Bargaja a bangare guda da kuma ’yan ta’adda a daya bangaren.
Da yake magana kan sabbin makamai da mayakan Turji, Basharu ya ce, bayanan leƙen asiri da aka samo daga Binchi sun nuna cewa na’urar gani a cikin dare da ake zargin Turji ya saya makon jiya tana cikin kayan aikin da aka kawo masa.
Ya yi zargin cewa Kachalla Haru Dole da Kachalla Ibrahim Chimo, wadanda ya bayyana a matsayin kwamandojin da ke jagorantar manyan sansanonin ’yan bindiga a bayan Kogin Maradun, suna da hannu wajen saye da kuma jigilar makaman.
Ya ce su biyun sun taka muhimmiyar rawa wajen saukaka isar da makaman ga Turji, lamarin da ke nuna karuwar hadin gwiwa tsakanin Chimo da Turji, wanda ya ce na iya zama wani bangare na dabarar fadada ayyukansu a fadin Gabashin Sakkwato.
Ya bayyana damuwa cewa wannan haɗin gwiwa na iya zama wani shiri na kai hare-hare a lokaci guda kan hedikwatar ƙananan hukumomi guda biyar a yankin kafin lokacin kololuwar damina.
Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su kara sa ido tare da daukar matakan gaggawa don tabbatar da sahihancin bayanan leƙen asiri da kuma hana duk wata barazana ga rayuka da dukiyoyi.