’Yan Boko Haram na kwararowa Nijeriya daga Chadi

Chadi ta fice daga rundunar hadin gwiwar kasashe masu yaki da Boko Haram, inda take ragargazar mayakan kungiyar suna tserewa zuwa sassan Nijeriya da Nijar

’Yan Boko Haram na kwararowa Nijeriya daga Chadi

Mayaƙan Boko Haram na tserewa zuwa kauyukan Njihar Borno da ke Nijeriya domin tsira da rayukansu sakamakon zaragazar su da sojojin Chadi suka tsananta.

Shugaban Chadi, Shugaba Mahmat Deby Itno, ya bayar da umarnin ne a fagen daga bayan yan ta’adda sun kashe sojoji 40 a ranar Lahadi a sansanin soji na Barkaram da ke yankin Tafkin Chadi.

Cikin fushi shugaban ya ba da sanarwar ficewar kasarsa daga rundunar hadin gwiwa ta kasashen Benin da Kamaru da Chadi da Nijar da Najeriya.

Harin bama-bamai daga sama da kasa, rahotanni sun ce a halin yanzu na tilastawa ’yan ta’addan yin kaura zuwa kauyukan da ke makwabtaka da Nijar da Najeriya.

Wani manomin da ya tsira daga harin ta’addancin da mayakan ta’addan suka kai musu ya ce mayakan suna yin garkuwa da mutanen kauyen suna neman a nuna musu hanyar tsira.

“Kwanan nan sun kama masuntanmu suka daure su da igiya, bayan sa’o’i da dama, sai suka sake su suka gudu,” in ji majiyar.

Ta ce ’yan Boko Haram da ke aika-aika a yankin Chadi suna guduwa zuwa kauyukan Nijar da Najeriya domin guje wa hare-haren bam da sojojin Chadi ke kaiwa.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce kauyuka irin su Mangari da Doron Nairada Malam Karanti da ke karamar hukumar Kukawa a jihar Borno na zama mafakar ’yan ta’addan da ke tserewa.

“’Yan ta’addan da suka tsere suna garkuwa da masuntan mu, suna neman a nuna musu hanyoyin tserewa a gabar kogin; suna kuma amfani da kwalekwalenmu wajen tsallaka koguna don gudun kada sojoji su riske su,” in ji shi.

Wani mamba na CJTF ya bayyana cewa ’yan ta’addan na kuma neman mafaka a kauyukan da ke kan iyaka da Nijar kamar Tunbun Bagudu da Gadira da Bulatigir da Lelewa.

Ya kara da cewa akwai bukatar sojojin Najeriya da na Nijar su kara kaimi a yankunan domin hana su sake haduwa domin sake kai wani hari.

Sanata Barau ya kai ziyarar ta’aziyya a Kano

Mun kusa kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya — Tinubu

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur