’Yan Boko Haram ne ke iko da iyakokin Najeriya a Arewacin Borno

A karshen makon jiya ne ’yan kungiyar Boko Haram suka kai kwace garin Baga bayn sun kai hari da wasu garuruwan da ke kusa a karamar Hukumar Kukawa da ke cikin Jihar Borno, inda suka kashe mutane da dama da kone dukiyoyi, inda fadawar garin hannunsu ya ba su damar iko da iyakokin Najeriya a […]

’Yan Boko Haram ne ke iko da iyakokin Najeriya a Arewacin Borno
’Yan Boko Haram ne ke iko da iyakokin Najeriya a Arewacin Borno

A karshen makon jiya ne ’yan kungiyar Boko Haram suka kai kwace garin Baga bayn sun kai hari da wasu garuruwan da ke kusa a karamar Hukumar Kukawa da ke cikin Jihar Borno, inda suka kashe mutane da dama da kone dukiyoyi, inda fadawar garin hannunsu ya ba su damar iko da iyakokin Najeriya a Arewacin Borno.

Wasu daga cikin mutanen da suka kubuta daga harin sun tsallaka zuwa kasashen Chadi da Nijar wasu kuma sun gudo Maiduguri.
Wakilinmu ya zanta da wadanda suka gudo Maiduguri a tashar mota ta Baga inda daya daga cikinsu Alhaji Gana ya shaida masa cewa, “Sun kawo mana hari da farko sun nufi jami’an tsaro domin akwai kayan aiki da aka kai musu ranar Jumu’a sai suka kai hari a sansanin sojojin hadin gwiwa suka kwashe kayan aikin, bayan da sojojin suka gudu. A gaskiya Boko Haram sun kashe mutane maza da mata mu ma kwananmu na gaba ne, domin kuwa muna gudu suna harbinmu da bindiga, muna kallo mutane na faduwa babu yadda za mu yi, har muka kawo Kuros Kauwa zuwa nan Maiduguri. Na ga wasu sojojin da suke cire kayan sarkinsu suka yar da makamansu suka gudu.”
Shi kuma Tasi’u Alhaji Hamza ya ce ’yan Boko Haram din sun kewaye garin ne tunda asuba babu ta inda mutum zai gudu, “Na hau kan itace ne har gari ya waye kafin in gudu, na ga gawarwaki a yashe a kasa, kuma na ga sojoji suna gudu wasu da kayansu na sarki wasu sun tube babu makamai a hannunsu.”
Malama Fatuma da gudo da ’ya’yanta kanana su uku, ta ce “Ni da ’ya’yana masu shekara biyur zuwa bakwai mun ratsa ne a daidai lokacin da Boko Haram ke harbe-harbe, kuma mun sha wahala ga tsoro da rashin kwanciyar hankali ga yunwa, kuma mun hadu da gawarwaki a hanya, amma muka yi karfin hali muka wuce.”
kwace garin Baga da mayakan Boko Haram suka yi, ya sanya daukacin kananan hukumomin da ke Arewacin Borno sun koma karkashin ikon kungiyar. Garin Baga shi ne na karshe da ke hannun gwamnati tun bayan da ’yan Boko Haram suka tsananta kai hare-hare a yankin.
Sanata mai wakiltar Borno ta Arewa, Alhaji Maina Ma’aji Lawal ya ce hare-haren sun jawo al’ummar yankin na zaune cikin mawuyacin hali.
“Abin bakin ciki ne gare ni, babu abin da zan ce sai dai in ba mutane hakuri,” ya shaida wa BBC, Landan.
kananan hukumomin da ke Arewacin Borno su ne Marte da Magumeri da Mobbar da Gubio da Guzamala da Abadam da Kukawa da Kaga da Nganzai da kuma Monguno.
Wani mazaunin garin Baga ya shaida wa BBC cewa “Dukan kan iyakokin Najeriya da Nijar da Kamaru suna hannun ’yan Boko Haram.”

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da sace dabbobi a Katsina  

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista