’Yan Boko Haram sun abauce
Yunkirin da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi don kawo karshen Boko Haram ya sanya’ya’yan kungiyar ta Boko Haram sun abauce suna ta kai hare-hare babu kakkautawa inda suka fara da kaddamar da hare-haren manyan rokokin harbo jiragen sama da na kunar bakin wake a Maiduguri, jim kadan da umarnin da Shugaba Buhari ya bayar na […]

Yunkirin da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi don kawo karshen Boko Haram ya sanya’ya’yan kungiyar ta Boko Haram sun abauce suna ta kai hare-hare babu kakkautawa inda suka fara da kaddamar da hare-haren manyan rokokin harbo jiragen sama da na kunar bakin wake a Maiduguri, jim kadan da umarnin da Shugaba Buhari ya bayar na a mayar da hedkwatar yaki da Boko Haram daga Abuja zuwa Maiduguri.
Sama da mutum 50 ne suka rasa rayukansu a hare-haren rokoki da na kunar bakin waken da ’yan Boko Haram din suka kai a gidaje da wani masallaci a garin Maiduguri a ranar Juma’a da Asabar din da suka gabata.
A ranar Juma’ar makon jiya wadanda ake zargi ’yan Boko Haram ne sun kai harin rokoki a Unguwar Dala Ngomari da daddare wadanda suka fada kan gidajen mutane suka hallaka sama da mutum10 tare da jikkata wasu, sannan washegari Asabar wani dan kunar bakin wake ya shiga masallaci ya tayar da bam a lokacin Sallar La’asar a Unguwar Makera Alin Kotoko kusa da Kasuwar Monday Market da ke Maiduguri, inda ya hallaka mutum 20 tare da jikkata wasu da dama.
Bugu da kari wani bam ya sake tashi a Tashar Alade a karamar Hukumar Hawul a ranar Asabar inda ya hallaka mutane da dama, sai kuma a ranar Litinin wata ’yan kunar bakin wake ta kashe kanta a garin Biu kafin ta karasa inda take nufin tayar da bam din da take dauke shi.
’Yan Boko Haram din sun sake jefa gurneti a Unguwar Ajilari da Dala Alajeri a cikin dare a ranar Litinin, amma bai hallaka kowa ba, sai dai ya rusa gidaje tare da ji wa wasu mutane rauni.
Kwana daya bayan harin kunar bakin wake da ya hallaka mutane a Maiduguri, wani bam din ya sake fashewa a birnin, inda ya hallaka mutum takwas a tashar Baga. Kuma wasu shaidu sun ce bam din ya jikkata mutane da yawa.Wani mazaunin birnin ya shaida wa sashin Hausa na BBC cewa “Mun ji karar mai karfin gaske da ya firgita mu lokacin da bam din ya fashe.”
Sai kuma wani harin bam din da aka sake kaiwa a Kasuwar Shanu (Mayanka) da misalin karfe 11:30 na safiyar Talata, inda ya hallaka sama da mutum 20. Shaidu sun ce wani mai tallar maganin gargajiya a kan keke ne wanda ya sanya wakar Janar Buhari a lokacin da ya tabbatar hankali ya koma kansa ne ya tayar da bam din.
Malam Ibrahim, wanda yana daya daga cikin ’yan kasuwar da bam din ya tashi a kan idonsa, ya shaidaw a wakilinmu cewa “Muna cikin tsakiyar cin kasuwa sai ga wani yana tallar maganin gargajiya a kekensa kuma ya sa wakar Janar Buhari, duk hankali sai ya koma kansa, ashe yana dauke da bam, kwatsam sai ya tada bam din ya kashe sama da mutum 20 har da shi, kuma ya jikkata wasu da dama. Duk da cewa ina da tazara da shi amma tartsastin bam din ya shafi na kusa da ni, ya kashe mutum biyu, amma babu abin da ya same ni, bam din ya kuma barnata wasu shaguna da hallaka dabbobi.”
Shi ko Malam Modu, wanda ya ce ya zo kasuwar ce don sayen nama abin ya rutsa da shi, ya ce ya tsorata sosai. “Na zo Kasuwar Shanu ne domin in sayi nama to amma sai na ga wani yana tallar maganin gargajiya tare da sanya wakar Shugaba Buhari, kawai sai na ji wani abu mai kara ya tashi ya kuma kashe mutane da dama, nan na ruga a guje, abin bai same ni ba, sai dai ya samu wasu abokaina,” inji shi.
Sai dai Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Borno Aderemi Opadokun wanda ya tabbatar da auikuwar harin ya ce mutum biyar ne har da dan kunar bakin waken suka mutu a harin na kwata, yayin da mutum takwas suka samu raunuka.
kungiyar Boko Haram ta kuma fitar da wani faifan bidiyo tana musanta ikirarin da sojojin Najeriya suka yi na samun nasara a kansu. Boko Haram ta fitar da sabon bidiyon ne a ranar Talata, sai dai bidiyon bai nuna hoton shugaban kungiyar Abubakar Shekau ba ko wanda ke magana da yawun kungiyar, a wani sako mai taken “Daular Musulunci a Afirka.”
Mai magana da yawun kungiyar da ba a nuna fuskarsa ba a sakon bidiyon ya kira Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar da ke fada da su a matsayin makaryata. A cikin sakon bidiyon na tsawon minti 10, kungiyar ta ce tana ci gaba samun nasara, har ma sakon bidiyon ya ce ta kakkafa makarantun koyon karatun Alkur’ani da cibiyoyin kera makamai a dajin Sambisa.