’Yan Boko Haram sun abodare *Sun kashe mutum 400 a kauyukan Gwoza *Sun kone daruruwan gidaje, sun kwashi abinci
daruruwan ’yan bindiga da ake zargin ’yan Boko Haram ne, a ranar Talata, suka abodare bayan da suka yi shigar sojoji suka kashe fiye da mutum 400 a kauyukan Attagara da Aghapalwa da kuma danjara da ke karamar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.Shugabannin jama’a da mazauna kauyukan sun ce ’yan bindigar sun kai harin daukar […]

daruruwan ’yan bindiga da ake zargin ’yan Boko Haram ne, a ranar Talata, suka abodare bayan da suka yi shigar sojoji suka kashe fiye da mutum 400 a kauyukan Attagara da Aghapalwa da kuma danjara da ke karamar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.
Shugabannin jama’a da mazauna kauyukan sun ce ’yan bindigar sun kai harin daukar fansa ne, kuma sun yi amfani da manyan bindigogi ga bama-bamai wajen kone kusan daukacin gidaje da shagunan kauyukan.
Wasu majiyoyi sun ce mutanen da aka kashe sun kai 500 a harin na baya-baya a Attagara, kuma an ce ya fi na Gamboru da ke Gabas maso Tsakiyar Borno, inda aka kashe kusan mutum 400, aka kone daruruwan gidaje da motoci fiye da 300 da babura da suka haura dubu daya.
Wakilinmu ya ruwaito cewa matsalar ta taso ne lokacin da mafarauta da matasa ’yan banga suka kashe ’yan Boko Haram hudu da ake zargi da kashe masu bauta a wani coci a ranar Lahadi. Kuma aka kama uku daga cikin wadanda suka yi kisa a cocin aka mika wa jami’an tsaro da ke Pulka, wani kauye mai dan girma da sojoji ke da sansani.
Wani shugaba a Attagara da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa an yi kisan gilla ga jama’arsa. “A yanzu da nake magana da kai, dubban gawarwaki suna warwatse a kauyukan Attagara da Aghapalwa da danjara da kuma Goshe, saboda babu wanda zai binne su. Kuma an kashe dagacin danjara; an kashe ’yan uwana maza biyar, daruruwan matasanmu sun kwanta dama. Muna fuskantar mummunan yanayi fiye da duk yadda jama’a ke tunani,” inji shi.
Ya ce a yayin harin, mata ne kawai aka bari, inda ya ce hatta kananan yara ba a bari ba. “Maharan sun rika kwace jarirai maza daga bayan iyayensu mata suna kashewa,” inji shi.
Shugaban al’ummar ya bayyana yadda maharan suka yaudari mutanen kauyukan uku inda suka taru a wuri daya kafin su kashe su. A cewarsa, “Bayan harin coci a Attagara a ranar Lahadi, labari ya watsu cewa ’yan Boko Haram suna shirin kai mana hari, don haka muka kasa barci. A ranar Talata mun je Pulka muka bayyana halin da muke ciki ga sojojin da ke can. Mun nemi taimakonsu, inda suka shaida mana kada mu damu. Sun ce mu koma kauyukanmu tare da ba mu tabbacin za a turo sojoji su kare mu daga yiwuwar kowane hari. Mun gaskata su muka koma.”
Ya ce, “Da misalin karfe 10 na safe, sai muka ga kimanin motocin soja a-kori-kura guda bakwai, wadanda muka dauka sojojin ne saboda dukkansu suna sanye da kakin soja da rigunan sulke da hulunan kwano da sauran kayan soja. Sai hankalinmu ya kwanta da muka gansu. Bayan sun iso sai suka nemi mutanemu su taru a wuri daya. Kamar yadda aka saba a wannan bangare na kasa, sai mata suka koma gefe daya, maza suna daya gefen. Da maharan suka lura daruruwan mutane sun hallara, sai shugabansu ya ce, ‘Allahu Akbar’ shi ke nan sai suka fara bude wuta ga bangaren da maza suke.”
Ya ci gaba da cewa: “Sai wurin ya hargitse inda maza da mata da yara suka rika gudun neman ceto ta yankunan duwatsu, amma sai wasu maharan suka fito a kan babura suna bin su suna harbi.”
Ya ce maharan sun ci karensu babu babbaka tun daga karfe 10 na safe har zuwa 5 na yamma ba tare da samun turjiya daga kowane bangare ba.
Ya ce, “Yau (shekaranjiya Laraba) ’yan ta’addan sun sake haduwa suka tafi kauyen Goshe, inda suka kashe mutane da dama, suka yi awon gaba da tumaki da awaki da daruruwan buhunan abinci, sannan suka kone daukacin kauyen.
Michael Isa na kauyen Goshe ya ce suna fuskantar bala’i, kuma bai san yadda aka yi ya tsira ba, amma ana yunkurin shafe mutanensu daga bayan kasa, inda mata kawai ake bari.
Ba wani jawabi da ya fito daga Rundunar Soja ta Bakwai ko ’yan sanda da ke Maiduguri game da harin na bayan nan.
kauyuka da rugage da dama ne aka wargaza a kananan hukumomin Gwoza da Bama da Konduga a ’yan makonnin nan, kuma harin na baya a zo ne kwana shida kacal da kashe Sarkin Gwoza Alhaji Idrissa Timta.
Gwoza dai ta yi iyaka da kasar Kamaru, kuma tana kewaye da dutsen Mandara da kuma dajin Sambisa da ’yan Boko Haram ke da sansani.