’Yan Boko Haram sun aika wa garin Chibok da takardar kai hari

kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram, ta aike da takardar gargadi mai cewa za ta kai wa al’mmar garin Chibok hari a kowane lokaci. Wani mazaunin garin Chibok din mai suna Martin Sani, ya ce “Na ga wannan takardar gargadin cewa za aka kawo mana hari […]

’Yan Boko Haram sun aika wa garin Chibok da takardar kai hari
’Yan Boko Haram sun aika wa garin Chibok da takardar kai hari

kungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram, ta aike da takardar gargadi mai cewa za ta kai wa al’mmar garin Chibok hari a kowane lokaci. Wani mazaunin garin Chibok din mai suna Martin Sani, ya ce “Na ga wannan takardar gargadin cewa za aka kawo mana hari kuma wannan abin bakin ciki ne kwarai. Muna rokon Allah Ya yi mana tsari da su, to, amma mun dauki wannan takarda mun kai wa ’yan sanda kuma sun ce suna aiki a kan takardar, amma mu a nan muna rokon hukumomi su yi wa Allah su kawo mana jami’an tsaro domin har yanzu garinmu na Chibok babu jami’an tsaro, don haka idan aka kawo jami’an tsaro to abin zai iya zama mana da sauki.”
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, DSP Gideon Jibrin, ya shaida wa wakilinmu cewa rundunar ba ta da labarin wannan takarda a yanzu, amma suna sauraron rahoton wannan takarda daga ofishinsu na yankin, amma duk da haka za su yi bincike a kai.
A wani labari kuma ’yan banga da aka fi sani da Sibiliyan JTF, sun kashe ’yan kungiyar Boko Haram 8 a kauyen Kwarangilam mai tazarar nisan kilomita 15 daga garin Chibok a Jihar Borno. Majiya mai tushe ta ce ’yan bangar sun yi wa maharan kwanton bauna ne da suka kai wa jama’ar kauyen hari da dare.
Shugaban ’yan banga na Jihar Borno Adamsi Tar ya ce maharan suna shammatan mutane ne su kai hari ba tare da sanin mutanen ba, to a wannan lokacin sun yi rashin sa’a “domin kuwa mun bullo musu ta inda ba su zata ba, a yayin da suke kokarin kawo wa kauyenmu hari, muka dakatar da su ta hanyar yi masu kwanton bauna, muka yi musu kofar rago har muka kashe mahara 8, tare da kwace makamansu,” inji shi.
Ya ce mutanensu sun yi amfani da makaman gargajiya don samun nasara a kan ’yan bindigar, duk da cewa maharan sun kone wasu gidaje da shaguna a kauyen da sauran wasu barna, sai kuma wasu daga cikin ’yan kungiyar sun rasa gidaje da kayan aikinsu. Shugaban ya ce “Za mu iya tunkarar ’yan ta’addan mu ci nasara a kansu, to amma kayan fadanmu irin na gargajiya ne ba zai yiwu mu yi fada da su ba alhali suna da kayan fada na zamani, saboda haka muna bukatar kayan fada na zamani da ababen hawa,” inji shi.
Wani mai magana da yawun ’yan bangar Muhammed Gaba, ya ce a daya daga cikin samamen da suka kai wa maharan mun sami nasarar cafke wani dan ta’adda daya sun mika shi ga jami’an tsaro.