’Yan Boko Haram sun fara amfani da mahaukata wajen kai hari
Wata da ake zargi ’yar kunar bakin wake da kuma ake zaton tana da tabin hankali ta kai harin kunar bakin wake a mashigar Babbar Kasuwar Damaturu a Jihar Yobe, inda ta yi sanadiyar rasa rayukan akalla mutum 19 tare da jikkata mutum 47. Wannan hari dai shi ne harin kunar bakin na uku a […]
Wata da ake zargi ’yar kunar bakin wake da kuma ake zaton tana da tabin hankali ta kai harin kunar bakin wake a mashigar Babbar Kasuwar Damaturu a Jihar Yobe, inda ta yi sanadiyar rasa rayukan akalla mutum 19 tare da jikkata mutum 47.
Wannan hari dai shi ne harin kunar bakin na uku a kasa da mako biyu da aka kai garin na Damaturu hare-haren da suka hallaka sama da mutum 42 tare da jikkata mutane masu yawa.
Malam Garba Yakubu wani dan banga da ke wurin da abin ya faru da ya ce Allah ne kawai Ya sa kwanansa na gaba, inda ya bayyana wa Aminiya cewa, yana wurin lokacin da ’yar kunar bakin waken ta zo da misalin karfe 10:00 na safe. Ya ce yana aikin lura da mutane sai ya ji jayayya ta kaure a tsakanin abokan aikinsa biyu wadanda dukkansu harin ya rutsa da su wato Garga Buba da wata mace da ke duba mata wato Ya-Mairam Falmata da kuma ’yar kunar bakin a kan ta ki yarda a duba ta. Ya ce yana kokarin yunkurowa don jin abin da ke faruwa ne sai ta tada bam din.
Garba Yakubu ya ce nan take ya fadi a kasa, da kura ta lafa ne sai ya gan shi cikin gawarwaki jina-jina, sai ya mike kasancewar ko kwarzane babu a jikinsa.
Wani mai sayar da kayan lokin da ke gab da isa wurin da abin ya faru, ya bayyana wa Aminiya cewa, “ya hango jama’a a tare a kofar shiga kasuwar ashe lokacin ana son bincika matar ce sai kawai ya ji kara mai karfi shi da kayan da yake dauke da su suka fadi
kasa daga bisani da komai ya lafa sai ya hango mutane jina-jina a kwakkwance.”
Kakakin Rundnar ’Yan sandan Jihar Yobe, ASP Toyin Gbadegesin ya tabbatar wa Aminiya cewa lamarin ya faru amma mutum 14 ne suka rasu, ya yin da mutum 47 suka jikkata, ya ce watakila a samu karuwar wadanda za su rasu don akwai daga cikin wadanda rauninsu ya yi tsanani.
ASP Toyin ya ce mace ta kai harin kuma tana cikin mutanen da suka rasu, kuma bayan kura ta lafa jami’ansu masu kunce bam sun kunce wasu bama-bamai biyar da ba su kai ga fashewa ba.
Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya yi Allah wadai da harin tare da jajanta wa iyalen wadanda harin ya rutsa da su kuma ya umarci jami’an Babban Asibitin Damaturu su kula da marasa lafiyar kyauta ba tare da an caje su ba.