’Yan Boko Haram sun fara gudu suna barin matansu
Mayakan kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin Arewa maso Gabas sun fara gudu suna barin matansu, sakamakon matsin da suke samu daga sojojin Najeriya bayan hawan mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.Wasu majiyoyi sun ce akalla mata ’yan Boko Haram 12 ne suka mika wuya ga ’yan kato da gora a karamar Hukumar Askira-Uba da […]
Mayakan kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin Arewa maso Gabas sun fara gudu suna barin matansu, sakamakon matsin da suke samu daga sojojin Najeriya bayan hawan mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wasu majiyoyi sun ce akalla mata ’yan Boko Haram 12 ne suka mika wuya ga ’yan kato da gora a karamar Hukumar Askira-Uba da ke Jihar Borno a ranar Litinin da Talatar da ta gabata.
Wani dan kato da gora da aka fi sani da Sibiliyan JTF a yankin mai suna Apagu Istifanus ya shaida wa kafar labarai ta Sahara Repoters cewa cikin matan har da mata biyu da suke dauke da ciki.
Y ace matan sun shaida musu yadda mazajensu suka gudu suka bar su saboda rashin abinci da man fetur.
An ruwaito Istifanus yana cewa: “A ranar Litinin hudu daga cikinsu (matan) sun zo Askira. Bayan dogon bincike sun shaida mana cewa mazajensu sun kasa ciyar da su, kuma suna da yawa a daji sannan akwai wadanda za su dada gudowa, an dauke su zuwa Biu don dada tatsar bayanai.”
Ya kara da cewa: “Jiya (ranar Talata) da misalin karfe 4:00 na yamma wasu mata takwas sun sake bayyana, biyu daga cikinsu dauke da ciki, mazajensu sun gudu sun bar su da ’ya’yansu a kauyen Ngulde da ke karamar Hukumar Damboa. Kuma mun mika su ga sojoji wadanda suka dauke su zuwa Mubi.”
dan kato da goran ya dora alhakin hakan kan nasarar da sojoji suka samu ta katse kai wa ’yan ta’addan makamai da abinci da man fetur da kuma yadda sosjojin suke tala rawar gani a ’yan watannin nan wajen yaki da su.
Wata majiyar soji da ta nemi a boye sunanta ta tabbatar da wannan labari, inda ta kara da cewa: “Kun gani ba mu bayyana yadda muke gudanar da ayyukanmu ga manema labarai, amma gaskiya ne cewa ’yan Boko Haram suna guje wa wutar da muke bude musu, saboda ko dai sojoji sun lalata sansanoninsu ko sun kwace su.”
A shekaranjiya Laraba Rundunar sojin saman Najeriya ta ci gaba da luguden wuta a kan mayaaan Boko Haram a dajin Sambisa.
Kakakin Rundunar Iya Kwamanda Dele Alonge ya fadi a wata sanarwa cewa an kaddamar da hare-hare a yankin Ngoshe da kuma Pulka, ta amfani da jiragen yaki wajen lalata kayayyakin Boko Haram, ciki har da wasu farantai da ake amfani da su wajen samar da wutar lantarki.
Hakan na zuwa ne kwana daya bayan da sojojin Najeriya suka yi ikirarin sake kwace iko da garin Gamboru Ngala da ke Jihar Borno, kamar yadda Kakakin Sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kuka-Sheka, ya bayyana. Ya ce yanzu haka dakarun suna ta kokarin tattaro kayan yaki da motocin sintiri da ’yan Boko Haram din suka gudu suka bari.