’Yan Boko Haram sun fara hada bam a jakar ’yan makaranta -Sojoji

Sojojin Hadin Gwiwa (JTF) da ke aikin samar da zaman lafiya a Jihar Kano sun bankado wani shiri na ’ya’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram na sanya bama-bamai a cikin jakunkunan da ’yan makaranta ke goyawa domin kai harin kunar baki wake.Kwamandan Birged din Soja […]

’Yan Boko Haram sun fara hada bam a jakar ’yan makaranta -Sojoji

Kayan hada bama-bama da soja suka kama a wannan mako a Kano. Sojojin Hadin Gwiwa (JTF) da ke aikin samar da zaman lafiya a Jihar Kano sun bankado wani shiri na ’ya’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram na sanya bama-bamai a cikin jakunkunan da ’yan makaranta ke goyawa domin kai harin kunar baki wake.
Kwamandan Birged din Soja ta 3 da ke Bukabu, Kano, Birgediya Janar Iliyasu I. Abba ne ya bayyana haka ga manema labarai, bayan da sojojin suka kai samame wasu gidaje da ake zargin ’ya’yan kungiyar suna zaune a kauyen Gunduwawa kimanin kilomita biyar daga birnin Kano a ranar Talatar da ta gabata.
Ya bayyana cewa jami’ansa sun kai mamaya kauyen na Gunduwawa ne bayan da suka samu rahoton sirri game da mutanen da ake zargi, ya ce amma kafin su isa sun sulale sun gudu.
Birgediya Abba ya ce a sakamakon samamen ne jami’ansa suka harbi wani dalibin sakandare mai suna Zuhairu Jibril inda ya rasu.
Ya ce a binciken da sojojin suka yi, sun gano kayayyakin hada bama-bamai da wasu da aka hada ciki har ma da wani bam da aka hada shi a cikin jaka irin ta ’yan makaranta.
Birgediya Abba ya bayayna cewa bincikensu ya gano cewa mutanen sun shirya kai hare-hare ne a yayin bikin Babbar Sallah mai zuwa da kuma sauran bukukuwan karshen shekara.
Da yake karin bayani Daraktan Hukumar Tsaro (SSS) a Kano, Mista Etang Bassey Etang ya ce yaron da aka harba yana tare da mutanen ne a gidan, inda yake kwana a gidan da aka samu wadannan bama-bamai. Sai ya gargadi jama’a kan su rika lura da sabuwar hanyar da ’yan kunar bakin wake suka fito da ita na goya jakar ’yan makaranta a baya, dauke da bam a cikinta.
Sojojin sun nuna kayan hada bama-baman da bam din da aka hada a cikin jakar goyawa a baya ta ’yan makarantar da abin matsawa don tayar da bam din. Sojojin sun ce wannan hanya ce sabuwa ta tashin bam-bamai a cikin taron jama’a.
A yayin harin, sojojin sun rusa wasu gidaje biyu da ke kusa da juna, ciki har da wanda suka harbe dan makarantar da ke kwana a cikin shagon da ke gidan.
Majiyarmu ta ce sojojin sun yi kutse a cikin dare da nufin rutsawa da mutanen da suke nema ne, sai dai kuma mutanen sun sulale, sai matansu biyar suka iske.
Mahaifin dalibin, Malam Jibril Abdullahi wanda shi ne mahaifin mai gidan da wadanda ake zargin suke haya, ya bayyana wa Aminiya cewa, “Da misalin karfe 2:00 na dare muka ji kukan motocin sojoji sun shigo unguwarmu, suka zo suka kewaye nan gidan a cikin motion yaki uku.”
Ya ce daga nan suka haye saman gidajen jama’a suka rika harbe-harbe, amma ba su taba kowa ba, suna jiran su samu mutanen da suke nema ne. Ya ce da suka gama harbin, suka bincika suka ashe mutanen sun gudu tun kafin su kai gare su, sai matansu kadai sojojin suka kama.
Malam Jibril ya ce “A gabanmu sojojin suke tambayar matan cewa sun taba kama su a wani lokaci can baya a Unguwar Ja’en, har sojojin suka ce sun ba matan kudi don su koma kauyensu, kuma matan sun amsa cewa eh, an yi haka.” Ya ce dansa Aminu ne mai gidan da wadanda ake zargi suke haya kuma kanensa Zuhairu yake kwana a shagon gidan. Ya ce bayan gari ya waye ne, sai shugaban sojojin ya kira shi ya shaida masa cewa ga dansa nan tsautsayi ya rutsa da shi, an kashe shi a kokarin harbin mutanen.
Mai gidan, Malam Aminu Jibril ya ce wani abokinsa ne ya hada shi da masu hayar, ya ce masa daya makanike ne, dayan kuma dan kasuwa. “Ban san mutanen suna aikata wani abu ba, sai da wannan al’amarin ya faru,” inji shi.