’Yan Boko haram sun fara yanke haddi a Yobe
’Yan Boko Haram sun fara yanke wa jama’a haddi a garin Buni Yadi da ke karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe, bayan da suka mayar da fadar Hakimin Buni Yadi matsuguninsu inda suka kafa tutocinsu a kan gidan.Wani mazaunin yankin da yu gudu zuwa Damaturu ya shaida wa Aminiya a shekaranjiya Laraba wanda ya bayyana […]
’Yan Boko Haram sun fara yanke wa jama’a haddi a garin Buni Yadi da ke karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe, bayan da suka mayar da fadar Hakimin Buni Yadi matsuguninsu inda suka kafa tutocinsu a kan gidan.
Wani mazaunin yankin da yu gudu zuwa Damaturu ya shaida wa Aminiya a shekaranjiya Laraba wanda ya bayyana haka, ya ce mayakan Boko Haram din “Sun harbe mutum biyu saboda shan taba sigari, sannan suka yi bulala 80 ga wani bisa zargin zama da matar da ba tasa ba,” inji shi.
Majiyarmu ta ce mayakan Boko Haram sun mayar da fadar Hakimin Buni Yadi, Alhaji Mukhtar Ali Gangaram, hedkwatarsu inda wasu daga cikin kwamadojinsu suka mayar da fadar wurin kwanansu.
Majiyar ta ce: “Sun mayar da fadar hakimin sansaninsu, sun kafa tutoci biyu dauke da rubutu cikin Larabci a kofar shiga fadar, masu dauke da makamai suna gadi kuma da damansu suna kwana a ciki.”
Majiyar ta kara da cewa, maharani suna kai-kawo a kan baburansu ba wata damuwa, kuma su ke gudanar da shingayen tsaron ababen hawa da ke garin.
Wani mazaunin garin ya ce maharani sun je gidansa suna yi masa wa’azi inda suka bukaci sanin dalilin da yake ci gaba da zama a garin.
“Rukunin mahara uku sun zo a lokuta daban-daban suna yi min irin wadannan tambayoyi, “Me ya s aka zabi zama a Buni Yadi? Shin kana tare da iyalanka,” inji shi.
Ya ce, washegari iyalansa sun shawarce shi ya bar garin ta yadda za su bi shi daga baya.
Idan za a iya tunawa jami’an tsaro sun gudu daga sansaninsu da ke yankin sakamakon hare-haren da aka kai musu wuraren zamansu lamarin da ya jawo ruguza gadar kwaya daya da ke hada Kudancin Yobe da fadar jihar da sauran sassanta.
Iyalai da dama a yankin sun nuna tsoron cewa jihar za ta fuskanci karancin abinci saboda gazawar manoma su gudanar da aikin noma a bana.
Haka ma mutanen garin Bara hedkwatar karamar Hukumar Gulani sun ce maharani sun karbe garin da sauran manyan garuruwa da suka hada da Bularafa.