’Yan Boko Haram sun jefa bama-bamai ga masallatai a Yobe
Wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari ga wasu masallatai a garin Potsikum inda suka hallaka masallata 12, kuma suka jikkata sama da mutum 20.Majiyarmu a Potikum ta ce, harin farko an kai ne ga wata cibiyar ’yan uwa Musulmi da ke Unguwar Sakafa da misalin karfe 7:40 […]
Wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari ga wasu masallatai a garin Potsikum inda suka hallaka masallata 12, kuma suka jikkata sama da mutum 20.
Majiyarmu a Potikum ta ce, harin farko an kai ne ga wata cibiyar ’yan uwa Musulmi da ke Unguwar Sakafa da misalin karfe 7:40 na yamma a ranar talata yayin da ake haramar fara Sallar Isha’i inda wani dan kunar bakin waken ya zo kamar Sallah zai yi ya dauki buta zai yi alwala, take ya tada bam din da yake dauke da shi ya hallaka kansa da wasu masu Sallah uku nan take, daga baya daya ya rasu.
Wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa maharin bisa ga alama ya labe a kusa ne sai da ya ga ana haramar Sallah ya lalabo kamar zai yi alwala sai ya tada bam din.
Ya ce bam na biyu ba nisa a tsakaninsa da na farko, a cewarsa suna wurin da aka tada bam din farko sai suka ji fashewar na biyu, inda nan da nan garin ya rude kowa ya fara gudu zuwa gida, daga baya jami’an tsaro suka fara korar jama’a.
Bam din na biyu ya fashe ne a masallacin kofar gidan Alkali Kalli da ke kusa da kofar fadar Mai martaba Sarkin Fika, inda maharin da ya zo cikin wata karamar mota ya jefa bam a cikin masallaci ana Sallar Isha’i ya gudu bam din ya hallaka mutum shida nan take daga baya mutum daya ya rasu, kuma mutum 20 suka jikkata.
Kafin harin na Potiskum wasu mahara sun kai mabambanta hare-hare a kauyen Katarko da garin Gujba inda suka hallaka mutum takwas tare da raunata wasu masu yawan gaske da kuma lalata wata babbar gadar motar da ta hada Kudancin jihar da fadar jihar da wasu sassan Jihar Borno.
Wani mazaunin Katarko da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa maharan sun je ne a kan babura da motar a kori kura tun misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Litinin kuma da zuwansu sai suka auka wa tungar jami’an tsaron JTF da ke garin suka tarwatsa su, sannan suka tarwatsa gadar garin daga bisani suka shiga cikin suka kashe wasu malaman addini a garin ta hanyar yankan rago ga mutum shida, sannan suka sace wani babban malamin mai suna Malam Sheriff Ali da matarsa da wasu mutum biyu masu suna Goni Kolo da Is’hak Alhaji Goni.
Wannan shi ne hari na baya baya da maharn suka kai wa garuruwan jihar, inda a watannin baya suka kai hare-hare a garuruwan Goniri da Buni Yadi da Buni Gari da Sasawa da Ngirbuwa da sauransu.
Duk kokarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin kakakin rundunar tsaro ta JTF Kyaftin Eli Lazarus kan hare-haren ya ci tura, inda ya ki daukar wayarsa lokacin da aka buga.