’Yan Boko Haram sun kai hari kan masu biki a Borno

Ana tsaka da wani bikin nadin sarauta da na daurin aure mahara suka bude wa mahalrta wuta

’Yan Boko Haram sun kai hari kan masu biki a Borno

Tsohon hoto.

Mutum daya ya rasu wasu da dama suka jikkata lokacin da mayakan Boko Haram/ISWAP suka kai hari a wajen wani bikin aure a kauyen Kindila da ke Askira Uba a Jihar Borno.

Wata majiya ta ce maharan, a cikin manyan motoci guda biyu, sun tare hanyar fita sannan suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sa mutane guje-guje domin tsira da rayukansu.

“Daga baya maharan sun kashe wani dan banga, mai suna Suleiman bayan sun tafi da shi. Daga bisani an gano gawarsa,” in ji majiyar.

Maharan sun kai farmaki kauyen ne ana tsaka da wani bikin nadin sarauta da na aure, suka bude wa mahalrta bikin auren wuta, a cewar majiyar nan ta Zagazola Makama.

A baya-bayan nan dai ’yan ta’adda sun tsananta kai hare-hare a kan fararen hula da wuraren shakatawa a Jihar Borno, lamarin da ya janyo asarar rayukan fararen hula da dama da ba su ji ba, ba su gani ba.