‘Yan Boko Haram sun kai hari N’Djamena

Firaministan kasar Chadi Payimi Kalzebe Deubet ya ce kasarsa na zargin kungiyar Boko Haram da kai wasu hare-hare biyu na kunar bakin wake a safiyar ranar Litinin, a N’Djamena, babban birnin kasar Chadi. Harin farko dai ya tashi ne a babban barikin jami’an tsaro ‘yan sanda, inda wani mutum da yake akan babur ya jefa […]

‘Yan Boko Haram sun kai hari N’Djamena
‘Yan Boko Haram sun kai hari N’Djamena

Firaministan kasar Chadi Payimi Kalzebe Deubet ya ce kasarsa na zargin kungiyar Boko Haram da kai wasu hare-hare biyu na kunar bakin wake a safiyar ranar Litinin, a N’Djamena, babban birnin kasar Chadi.

Harin farko dai ya tashi ne a babban barikin jami’an tsaro ‘yan sanda, inda wani mutum da yake akan babur ya jefa wani bam. kasa da mintuna 30, sai aka sake jin karar fashewar wani abu a kwalejin horar da jami’an tsaro ta ‘yan sanda.
Ministan Kula da Harkokin Cikin Gidan kasar, Abderahim Biremé Hamid ne ya tabbatar da aukuwan wannan lamari bayan faruwarsa. Wannan ne karo na farko da birnin N’Djamena, ya fuskanci harin ’yan kunar bakin wake tun lokacin da kasar Chadi ta fara taimakawa wajen yaki da ta’addanci a farkon bana.
Jam==n tsaro da suka hada da dakarun Shugaban kasa, da kuma sojoji hadi da ’yan sanda sun yi wa birnin da’ira domin kara karfafa tsaro da kuma bin sawun wadanda ake tuhuma da aikata wannan aiki da kuma bincika ko akwai wasu ababan fashewar da aka boye a cikin birin.
Wadannan suna cikin matakan karfafa tsaron farko da Firaministan kasar ya dauka, inda yake cewa: “Za a kewaye birnin N’Djamena kuma a gudanar da bincike. Duk wani wanda ake zarge da aikata ba daidai ba, zai shiga hannun hukuma. Sa’annan kuma za a bi sawun duk wasu masu yawo a cikin motoci masu bakaken tagogi. Baya ga haka kuma za a sake karfafa matakan tsaro a gidajen shan mai, da matatun danyen man fetur, da filin jirgin sama, hadi da gadoji, da masallatai da kuma coci. Har ila yau, a makarantu da kasuwanni za a karfafa musu tsaro,” inji shi. Hakazalika, an haramta wa mata sanya nikabi a duk fadin kasar.
karin matakan da aka dauka sun hada da rufe hanyoyin motoci da suka dangana ta gaban fadar shugaban kasa da kuma babban barikin jami’an tsaron ’yan sanda, wurin da aka kai harin farko. Har ila yau, an dakatar da shiga da fice a tsakanin iyakar kasar Kamaru da Chadi ta birnin Kousseri, mai makwabtaka da N’Djamena.
A jiya Alhamis ne kuma rundunar sojin kasar Chadi ta ce ta kai hare-haren ta sama a kan sansanonin ’yan Boko Haram da ke Najeriya, domin daukar fansar hare-haren kunar bakin wake da ake zargin ‘yan kungiyar sun kai N’Djamena.
Firaministan ya ce cikin mutane 28 da suka mutu akwai mata hudu, da kuma ’yan kunar bakin wake hudu, sai mutane 100 da suka ji rauni.
A nashi bangaren kakakkin Gwamnati, Minista Hassan Sylla Bakary ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, saboda hukumomi suna ci gaba da daukar matakan da suka kamata. Hakazalika,Shugaban kasar Faransa ya ce kasarsa za ta taimaka wajen yaki da kungiyar Boko Haram.