’Yan Boko Haram sun kai hari yankin Tarmuwa

Wasu maharan kungiyar Boko Haram sun kai manyan hare-hare a garin Babban-Gida hedikwatar karamar Hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe inda suka haddasa asarar dukiyoyi da salwantar ran mutum daya. Wata majiya da ke garin ta bayyana wa Aminiya cewa maharan da ba su wuce 20 ba sun je garin ne a kan babura 10 da […]

’Yan Boko Haram sun kai hari yankin Tarmuwa
’Yan Boko Haram sun kai hari yankin Tarmuwa

Wasu maharan kungiyar Boko Haram sun kai manyan hare-hare a garin Babban-Gida hedikwatar karamar Hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe inda suka haddasa asarar dukiyoyi da salwantar ran mutum daya.

Wata majiya da ke garin ta bayyana wa Aminiya cewa maharan da ba su wuce 20 ba sun je garin ne a kan babura 10 da misalin karfe 6.00 na yammacin ranar Asabar da kasuwar garin ke ci.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaye sunansa ya shaida wa Aminiya ta wayar salula cewa, tun misalin karfe 3.00 na yamma aka fara samun rahoton cewa maharan na kan hanyarsu ta kai hari garin, wanda hakan ya sa jama’a da dama da wadanda suka zo cin kasuwa suka fara tserewa daga garin.
Ya kara da cewa, duk da samun wannan labari na yiwuwar kawo harin bai sa jami’an tsaron da ke garin sun yi wani yunkuri don kawar da shakka daga jama’a ba, inda ana gab da fara Sallar Magriba sai aka fara jin karar harbe-harben bindigogi, jama’a fara guje-guje zuwa daji don tsira da rayukansu.
Ya ce nan da nan ya dauki ’ya’yansa biyu a kan babur zuwa wani kauye mai nisan kilomita 10 a hanyar Jajere suka samu mafaka.
Wani ma’aikacin karamar hukumar mai suna Abdul Muhammad ya shaida wa Aminiya cewa, ya ga lokacin da maharan suka shiga garin bayan sun kai hari garin Mafa, kuma daga shigarsu garin suka fara harbe-harbe da kone gine-ginen gwamnati ba tare da fuskanci turjiya ba, saboda jami’an tsaron da ke garin sun sulale sun gudu ba tare an fafata da su ba.
Ya ce, ya boye ne a wani gida kuma da misalin karfe 9:00 na dare ne sai suka ji an yi tsit, alamar maharan sun bar garin, to, amma bai samu fita ba sai da safe, lokacin da jama’a
suka fito don gane wa idonsu irin barnar da maharan suka yi.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin jami’an tsaron JTF ya ci tura, amma Shugaban karamar Hukumar Tarmuwa Alhaji Sama’ila Mai Adamu ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun barnata wani sashi na ginin karamar hukumar da wani sashi na gidan Mai martaba Mai Jajere da babban ofishin ’yan sandan garin da sansanin rundunar JTF da sauransu, amma babu asarar rayuka ko jikkata. Ya ce al’amuran yau da kullum sun dawo a cikin garin.

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da sace dabbobi a Katsina  

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista