’Yan Boko Haram sun kai wa ayarin Gwamna Shettima farmaki
A daren Talatar da ta gabata ce wadanda ake zargin ’yan Boko Haram ne suka kai wa motoci shida daga ayarin Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno farmaki. Al’amarin ya faru ne a kan titin iyaka da Gamboru a Karamar Hukumar Ngala a Jihar Borno. An samu rahoton mutuwar mutum uku daga cikin ayarin Gwamnan […]
A daren Talatar da ta gabata ce wadanda ake zargin ’yan Boko Haram ne suka kai wa motoci shida daga ayarin Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno farmaki. Al’amarin ya faru ne a kan titin iyaka da Gamboru a Karamar Hukumar Ngala a Jihar Borno.
An samu rahoton mutuwar mutum uku daga cikin ayarin Gwamnan kuma wadansu da dama sun bata. Motocin shida dai, su ne jerin karshe na ayarin Gwamnan, a kan hanyarsu ta zuwa yakin neman zabe. Wata majiya ta shaida wa wakilanmu cewa an farmaki mutanen ne a yayin da suke hanyarsu ta zuwa garin Ngala.
Majiyar ta bayyana cewa, maharan sun bude wa motocin wuta ne, bayan da motocin da ke dauke da Gwamna suka wuce. Majiya mai tushe ta ce mutum uku ne suka rasa rayukansu a wannan farmaki.
“Mun samu rahoton labarin abin takaicin da ya faru a jiya, inda ’yan Boko haram suka kai wa ayarin Gwamna Shettima farmaki, suka bude wuta ga magoya bayan Jam’iyyar APC, kodayake harin bai rutsa da motocin da ke dauke da Gwamnan ba, amma wadanda harin ya rutsa da su, magoya bayanmu ne.
“Mun rasa akalla mutum uku kuma wadansu da dama sun samu raunuka kuma wadansu da dama sun bace, a yanzu da nake magana da kai, ba mu san inda suke ba,” inji daya daga cikin mambobin Jam’iyyar APC.
Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Usman Mamman Durkwa ya shaida wa manema labarai cewa shi ma ya ji batun amma ya kasa samun wayar ayarin Gwamnan, amma yana nan yana jiran tarbarsu.
Kakakin Runduna ta 7 ta Sojin Najeriya, Kanar Ado Isa ya ce, zuwa lokacin da yake magana, bai samu rahoton komai daga sojojin da ke yankin da al’amarin ya faru ba.
Haka kuma, an samu bayanin cewa maharan sun kwace motoci 8 dauke da mutane, cikinsu har da wani Babban Sakatare daHakimai uku na garuruwan Rann da Dikwa da kuma wadansu daga cikin ’yan bangar sa-kai na JTF.
Shugaban Karamar Hukumar Kala Balge, Nishad Lawan Musa ya bayyana wa manema labarai a Gamboru cewa ’yan ta’addar sun kai wa mutanensu hari su ma, inda ya kara da cewa har ma sai da suka kona motar sakatarensa.
Wata majiya daga bangaren jami’an tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa, tunda dadewa sun ba Gwamna Shettima shawarar cewa, bisa la’akari da kiyaye tsaronsa, ya kamata ya rika amfani da mota mai sulke, tunda akwai guda biyu da ke aje a ofishinsa amma ya ki.
“Motocin masu sulke, ana amfani da su ne kawai lokacin da za a yi wa wani babban jami’i rakiya a cikin Jihar Borno, don haka bai dace ba a matsayinsa na shugaban da ke jagorancin ayarinsa ya kasance cikin mota mai sulke, alhali mukarrabansa suna cikin motocin da ba masu sulke ba, suna yi masa rakiya. Shi a ganinsa, Gwamna ya ga bai dace ba, domin hakan na iya saka tsoro ga zukatan mukarrabansa da ke tare da shi,” kamar yadda wata majiya ta bayyana.