’Yan Boko Haram sun karbe Mubi
Mayakan Boko Haram sun karbe garin Mubi gari na biyu mafi girma a Jihar Adamawa, inda suka kashe sojoji tare da sake daruruwan fursunoni daga gidan kurkuku. Wata majiyar tsaro wadda ta tabbatar wa Aminiya asarar rayuka a tsakanin bangarorin soja da na maykan Boko Haram da kuma cewa sojoji sun gudu daga garin bayan […]
Mayakan Boko Haram sun karbe garin Mubi gari na biyu mafi girma a Jihar Adamawa, inda suka kashe sojoji tare da sake daruruwan fursunoni daga gidan kurkuku.
Wata majiyar tsaro wadda ta tabbatar wa Aminiya asarar rayuka a tsakanin bangarorin soja da na maykan Boko Haram da kuma cewa sojoji sun gudu daga garin bayan musayar wutar da ta dauki awanni a garin ta ce, ba za a iya kididdige yawan wadanda suka rasu a harin ba, amma mayakan Boko Haram din sun kashe fararen hula biyar.
“Wasu sojoji sun rasa rayukansu, kamar yadda maharan suka rasa, amma maharan sun samu galaba kan sojojin inda suka kwace iko ga garin,” inji majiyar.
Wani ma’aikacin jin kai a Mubi ya shaida wa Aminiya, cewa mayakan sun gudanar da jerin gwano a manyan titunan garin a kan babura da a kori kura da dama da wasu tankokin yaki kadan suna daga hannuwa ga jama’a don murnar samun nasara.
Ya ce,wasu daga cikin mayakan sun tabbatar da mutanen garin cewa ba za su cutar da sub a, amma suna da zabin barin garin idan suka ga dama,a cewarsa mazauna garin sun kidime inda daruruwa suka gudu cikin daji.
Ya ce, “Sun amshe barikin soja, sun kone wani caji ofis din ’yan sanda, kuma sun saki fursunoni. Za ka rika jin ana daga murya, mayakan ne suka jawabi ga jama’a a kan titi, amma muna cike da tsoro, saboda ba mu san abin da zai biyo baya ba.”
Wata majiya ta kusa da Fadar Sarkin Mubi ta ce an dauke iyalan Sarkin zuwa garin Dumo da ke kasar Kamaru don kare lafiyarsu, yayin da mafi yawan ’yan majalisar sarkin suka bar garin da safiyar shekaranjiya Laraba.
Kakakin Birged na 23 na sojojin Najeriya da ke Yola, ya ce sojoji ba za su iya tabbatar da faduwar Mubi ga mayakan Boko Haram ba, domin bai samu wani bayani a kai ba.
Gidan rediyon BBC, Landan ya ce bayanai sun nuna mayakan kungiyar Boko Haram sun kafa tutarsu a garin Mubi, kuma sun kafa dokar hana fita ko shiga garin, sannan a bangare guda kuma an datse layukan waya, lamarin da ya munana harkar sadarwa.
Wani dan garin Mubi, Malam Ahmed Sajo ya shaida wa BBC cewa lamarin ya ritsa da ’yarsa da iyayensa, wadanda ya ce ya daina jin duriyarsu.
Kafin su isa Mubi mayakan Boko Haram sun auka wa garin Uba a karamar Hukumar Askira a tsakanin jihohin Borno da Adamawa, kuma tuni jama’a da dama sun fice daga garin.
Kawo yanzu babu cikakken bayani a kan yawan mutanen da suka jikkata, amma wasu rahotanni sun ce tun a daren ranar Talata ne aka yi ta jin karar fashe-fashen abubuwa a garin Uba.
A ranar Litinin mayakan Boko Haram sun kai hari a karamar Hukumar Kukawa da ke Jihar Borno, a daidai lokacin da mutanen garin ke cikin kasuwa, kuma maharan sun kai hari a ofishin ’yan sandan yankin tare da kashe mutane da kone shaguna da motoci da
kuma sace dabbobi da kayan abinci.
Hukumomin jihar sun tabbatar da aukuwar lamarin da kuma sace mutanen da maharan ke yi a daidai lokacin da hukumomin tsaro a Najeriya ke cewa suna tattaunawa da kungiyar Boko Haram da nufin tsagaita wuta tare da sako wadanda maharan suka yi garkuwa da su ciki har da ’yan matan Chibok da suka sace sama da wata shida.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Hedkwatar Tsaro Manjo Janar Chris Olukolade bai amsa sakon tes da aka aika masa kan rahoton kame garin Mubi da Uba da mayakan Boko Haram suka yi ba.