’Yan Boko Haram sun kashe manoma 15 a Borno

Boko Haram ta kashe manoma 15 a Borno

’Yan Boko Haram sun kashe manoma 15 a Borno

Mayakan Boko Haram

Ana fargabar cewa mayakan Boko Haram sun kashe wasu manoma akalla 15 a kauyuka biyu na Karamar Hukumar Jere da ke Jihar Borno.

Bayanai sun ce ’yan ta’addan sun kai farmaki kauyen Kofa da tsakar dare, inda suka shafe kusan sa’a guda suna harbe-harbe a ranar Juma’a.

Wakilinmu ya rawaito cewa maharan sun yi wa wasu manoma yankan rago a kauyukan Molai Kura da Molai Gana, lamarin da wasu mazauna yankin da dama suka tsere cikin daji domin neman mafaka.

Wani jigo a kungiyar ’yan banga, Bukar Ali Musty, ya ce an kuma kai wa wasu manoman hari ne yayin da suke aikin gona.

A cewarsa, manoman na aiki ne a gonakinsu da ke kusa da Molai, a wajen birnin Maiduguri a ranar Alhamis din da ta gabata, inda ’yan tada kayar baya suka kai musu hari tare da sare musu kai.

“Akalla gawarwaki 15 ne aka kwashe a safiyar yau, an kai hare-haren ne ranar Alhamis.

“An sare kawunan manoma bakwai a lokacin da suke aiki a gonakinsu sannan maharan sun kuma yanke makogwaron wasu fararen hula takwas marasa lahani a gidajensu,” in ji shi.

Wani jami’in JTF da ke cikin tawagar da aka kwashe, ya nuna damuwarsa kan hare-haren, yana mai cewa dole ne duk masu ruwa da tsaki su farka don ganin ba a ci gaba da faruwa ba.

“Abin takaici ne dangane da ci gaba da faruwar hakan musamman a wannan lokaci na fara samun ruwan sama idan aka yi la’akari da ci gaban da muka samu a cikin watanni ba tare da an kai wa al’umma hari ba.

“Ina can da safe. Ba zan iya tunanin ganin an yanka ’yan uwana kamar rago ba dukkanin gawarwakin da muka kwaso an same su ne a cikin jini, kuma ina ganin dukkanmu muna bukatar mu tashi tsaye domin tunkarar wannan makiyin zaman lafiya,” in ji majiyar.

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele