’Yan Boko Haram sun kashe mutum 16 a Bosso

Wasu mazauna garin Gogole da ke Bosso a Jamhuriyar Nijar sun ce ’yan Boko Haram sun kai hari garin shekaranjiya  Laraba da daddare, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.Kodayake, sun ce ba-ta-kashin da aka yi tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da ‘yan kato-da-gora a garin, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 16. […]

’Yan Boko Haram sun kashe mutum 16 a Bosso
’Yan Boko Haram sun kashe mutum 16 a Bosso

Wasu mazauna garin Gogole da ke Bosso a Jamhuriyar Nijar sun ce ’yan Boko Haram sun kai hari garin shekaranjiya  Laraba da daddare, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
Kodayake, sun ce ba-ta-kashin da aka yi tsakanin mayakan kungiyar Boko Haram da ‘yan kato-da-gora a garin, ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 16. Har lokacin hada wannan rahoton dai babu cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru.
kungiyar Boko Haram ta tsananta kai hare-hare a Bosso da wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar tun daga farkon wannan shekarar, inda aka sanya dokar ta-baci a yankin Diffa.
Shugabannin kasashen da ke yankin Tafkin Chadi sun kafa rundunar da za ta murkushe mayakan kungiyar, sai dai har yanzu kungiyar na ci gaba da kai hare-hare.
Hakazalika, a farkon makon nan ne gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta soke bikin nunin tufafin gargajiya da ake yi a birnin Yammai kowace shekara saboda fargabar hare-haren ’yan ta’adda.
Baje kolin tufafin Afirka na FIMA dai na daga cikin muhimman bukukuwan nuna al’adu da ake yi a kasar.