’Yan Boko Haram sun kashe mutum 20 a masallaci
Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutum 20 a wani hari da suka kai ga wani masallaci a lokacin da mutane ke cikin Sallah a garin Buni Gari da ke karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe.Maharan sun yi amfani da bindigogi da bama-bami a yayin harin inda […]
Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan kungiyar Boko Haram ne sun kashe mutum 20 a wani hari da suka kai ga wani masallaci a lokacin da mutane ke cikin Sallah a garin Buni Gari da ke karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe.
Maharan sun yi amfani da bindigogi da bama-bami a yayin harin inda suka kone gidaje sama da 100 da motocin hawa kimanin 42 a kauyen.
Wata majiya a garin na Buni Gari da bai wuce kilomita 5 ba daga garin Buni Yadi hedikwatar karamar hukumar ta shaida wa Aminiya cewa maharan da suka zo a ranar Asabar da misalin karfe 6:45 na yamma lokacin da al’ummar Musulmin garin ke gab da fitowa daga masallaci bayan Sallar Magriba, sun yi tsinke ga masallacin ne inda suka shaida wa mutanen da ke cikin masallacin cewa a yau za su yi ramukon gayya kan mika wasu ’yan kungiyarsu uku da al’ummar garin suka yi ga jamai’an tsaron JTF, nan take suka yi ta harbe masallatan tare da jefa bama-bamai a cikin masallatan.
Malam Abubakar wani mazaunin Buni Gari da ya sha da kyar ya ce, maharan suna da yawa kuma sun zo ne a kan babura da motoci suka rika harbin kan mai uwa da wabi, kuma bayan da suka kashe masallatan ne sai suka rika banka wuta a gidajen jama’a da shaguna suka kone ilahirin motocin da suka ci karo da su a garin.
Ya ce, maharan sun rika cewa sun zo ne da nufin daukar fansa kan abin da mutanen garin suka musu na mika mutanensu ga dagutai don haka su ma sai sun dandana kudarsu, kuma in suka sake dawowa garin za su bi su yayyanka duk wanda suka samu ne kawai.
Kwamsinan ’Yan sandan Jihar Yobe Alhaji Sunusi A. Rufa’i ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce mutum 10 ne maharan suka kashe a masallacin duk da cewa wasu da yawa sun tsira da harbin bindiga, sai dai akwai yiwuwar samun karin rasuwar wasu daga cikinsu, ya kuma tabbatar da kone gidaje da abubuwan hawa masu yawa.
A ziyarar jaje da ya kai ga al’ummar garin Buni Gari a madadin Gwamna Ibrahim Gaidam, Mataimakin Gwamnan Jihar Injiniya Abubakar Ali ya yi nuna alhininsa game da wannan aika-aika, kuma ya umarci hukumar agajin gaggawa ta jihar SERA ta hanzarta kai kayayyakin tallafin ga al’ummar da harin ya rutsa da su ya kuma ce a yi kiyasin asarar rayuka da dukiyar da aka yi don daukar mataki a kai.