’Yan Boko Haram sun kashe mutum 51 a kauyukan Yobe da Borno
’Yan sanda a Jihar Borno sun tabbatar da cewa ’yan bindiga da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun harbe akalla mutum 42 a harin da suka kaddamar a Biu da Hawul da ke Jihar Borno. Mazauna yankin sun ce maharan sun je kauyukan Debiro Hawul da Debiro Biu a kan saman babura da mota […]
’Yan sanda a Jihar Borno sun tabbatar da cewa ’yan bindiga da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun harbe akalla mutum 42 a harin da suka kaddamar a Biu da Hawul da ke Jihar Borno.
Mazauna yankin sun ce maharan sun je kauyukan Debiro Hawul da Debiro Biu a kan saman babura da mota a kori kura a ranar Litinin inda suka bude wuta tare da kone gidaje da wawure dukiyoyin jama’a.
Rahotanni sun ce yara mata ke kai harin abin da ke dada jefa tsoro a cikin al’umma a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin murkushe mayakan Boko Haram din.
Akalla mutum 30 suka rasu a harin kunar bakin waken da akem zargin wata mace ta kai Kasuwar Kifi ta Tashar Baga da ke garin Maiduguri.
Shaidun sun ce harin baya ga hallaka mutane da jikkata wasu, ya kuma barnata dukiya ta miliyoyin Naira.
Wani dan kasuwar, Malam Sani Maikifi, ya shaida wa Aminiya cewa “Muna cikin Sallar La’asar sai muka ji karar bam a kusa da masallacinmu, Allah Ya sa bai tabe mu ba, amma ya shafi wasu abokan kasuwancinmu kuma wasu sun mutu, wurin kasuwancinmu ya lalace kai abin ba a cewa komai.”
Sakataren ’Yan Kasuwar Kifin, Hassan Baba Yerwa, ya ce akalla mutum 35 suka rasu kuma akasarinsu wadanda suke Sallah ne.
Wani dan kasuwa mai suna Ja’afar Aliyu, ya ce ’yar kunar bakin waken ta yi zo ne kamar mai sayayya a kasuwar, ta tsaya a kusa da babban Masallacin Juma’a a wajen kasuwar ana Sallar La’asar, inda ta tayar da bam a wajen masallacin ta kashe mutane.
Sai dai Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mista Adeniran ya ce mutum 12 ne suka rasu a harin.
A Jihar Yobe kuwa wata ’yar kunar bakin wake ce ta hallaka mutum 16 tare da jikkata 22 a kasuwar garin Nannawaji/Wagir a karamar Hukumar Gujba.
Wani ganau da ya tsallake da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar wa Aminiya cewa wata karamar yarinya da shekarunta ba su wuce 12 ba ne ta tada bam din a kusa da kasuwar hatsi da misalin karfe 11.00 na safe bayan wani mai babur ya zo ya ajiye ta. Ya ce nan take ta hallaka mutum 12 daga bisani yawansu ya kai 16, sai mutum 21 da suka jikkata.
Shugaban karamar Hukumar Gujba Alhaji Kyari Bataramma ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin inda ya ce, ana yi wa wadanda suka jikkata magani kyauta kamar yadda gwamnatin jihar ta ba da umarni.