’Yan Boko Haram sun kashe mutum shida a Adamawa
An kashe akalla mutum shida tare da kone gidaje da shaguna cikin dare a ranar Talata a garin Maidu da ke karamar Hukumar Madagali da ke Jihar Adamawa. Kwamishinan Watsa Labarai da Tsare-Tsare na Jihar Alhaji Ahmed Sajoh ya bayyana hakan a shekaranjiya Laraba a taron da aka yi don makiyaya a jihar. Alhaji Ahmed […]

An kashe akalla mutum shida tare da kone gidaje da shaguna cikin dare a ranar Talata a garin Maidu da ke karamar Hukumar Madagali da ke Jihar Adamawa.
Kwamishinan Watsa Labarai da Tsare-Tsare na Jihar Alhaji Ahmed Sajoh ya bayyana hakan a shekaranjiya Laraba a taron da aka yi don makiyaya a jihar.
Alhaji Ahmed Sajoh ya ce sojoji da ’yan sanda sun dora alhakin harin a kan ’yan Boko Haram, kuma sun tabbatar da cewa an rasa rayuka shida a harin, sannan an ci nasara kashe dan ta’adda daya.
“Bisa ga bincike da muka yi daga sojoji da ’yan sanda da mutanen garin sun tabbatar da rasa rayukan mutum shida a harin an kuma ci nasarar kashe dan ta’adda daya,” inji shi.
Ya ce sojoji da maharba da ’yan sa kai a fannin tsaro sun fatattaki maharan daga garin, kuma mutanen garin da suka watse zuwa wasu kauyuka ana kyautata zaton su dawo.
Kwamishinan Noma, Alhaji Ahmed Waziri ma ya tabbatar wa manema labarai faruwar harin a garin Maidu. Ya ce ga alama mutanen da suka kai harin suna cikin halin kunci kuma suna neman abinci da wasu abubuwan da za su gudanar da rayuwarsu.
Yayi kira ga gwamnatin jihar da ta tarayya da kada su gaji wajen tallafa wa harkokin tsaro don kare rayukar mutanen bangaren.
Da Aminiya ta tambaye shi kan daukin da sojojin da suke Gulak da Madagali, ya ce bai yi magana da su ba, amma ya yi magana da Shugaban karamar Hukumar Madagalin wanda ya ce yana hanyarsa ta zuwa garin kuma ya ce sojojin na samun labarin hari suka gaggauta kai dauki har suka kashe daya daga cikin maharan suka fatattaki sauran.