’Yan Boko Haram sun kashe Sheikh Misra yana ruku’u

Yan bindigar da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe wani fitaccen malamin Musulunci mai suna Sheikh Adamu Muhammad Misra. Marigayin, wanda ya fito daga tsatson Sheikh Muhammad Adam Nafada Al-Futy wata majiya ta shaida wa Aminya cewa ’yan bindigar sun kashe malamin ne yana cikin ruku’u a garin Nafada a ranar Talata.Sheikh Adamu […]

’Yan Boko Haram sun kashe Sheikh Misra yana ruku’u
’Yan Boko Haram sun kashe Sheikh Misra yana ruku’u

Yan bindigar da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe wani fitaccen malamin Musulunci mai suna Sheikh Adamu Muhammad Misra.

Marigayin, wanda ya fito daga tsatson Sheikh Muhammad Adam Nafada Al-Futy wata majiya ta shaida wa Aminya cewa ’yan bindigar sun kashe malamin ne yana cikin ruku’u a garin Nafada a ranar Talata.
Sheikh Adamu Nafada na daya daga cikin aminan Sheikh dahiru Usman Bauchi, kuma ya bude zawiyoyi sama da dubu daya kamar yadda majiyar ta shaida wa Aminiya.
Tuni Gwamnatin Jihar Gombe ta ba da umarnin rufe makarantun boko a jihar sakamakon hare-hare a garuruwan Nafada da Ashaka da Bajoga da ke jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ce iyayen yara da suka kai ’ya’yansu makaranta a shekaranjiya Laraba sun tarar da makarantun a rufe, saboda sun bi umarnin gwamnati.
Bayanai sun ce a ranar Talata da yamma ne gwamnati ta aike wa daukacin makaratu a jihar rubutaccen umarnin su rufe makarantun.
A wani labarin tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nemi kasashen duniya su taimaka wa Najeriya domin shawo kan matsalar tabarbarewar tsaro da take fuskanta.
A wani taron manema labarai da ya kira a Abuja, tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana takaicinsa dangane da irin mawuyacin halin da dubban mutane a shiyyar Arewa maso Gabas ke ciki, sakamakon hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa.
Alhaji Atiku Abubakar wanda wasu ’yan Majalisar Dattawa da suka fito daga yankin Arewa maso Gabas suka rufa wa baya a wajen taron, ya ce matukar ba a tashi tsaye ba, mayakan kungiyar Boko Haram na iya mamaye daukacin kasar nan baki daya.
Don haka ya bukaci ’yan Najeriya su nemi gwamnati da ta kara yin hobbasa don shawo kan matsalar ta Boko Haram. Ya ce, idan kuma gwamnatin ba za ta iya ba, to kuwa ya kamata ta san inda dare ya yi mata.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi