‘Yan Boko Haram sun kashe sojoji 3 da fararen hula 8 a Monguno
Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji uku da wasu fararen hula takwas tare da raunata wasu da dama a garin Monguno da ke jihar Borno, bayan sun kutsa cikin dakarun sojojin da wata mota mai dauke da bamabamai. Wannan harin na zuwa ne bayan kwanaki 10 da janye sojojin Chadi da ke taimakawa takwarorinsu wajen […]
Mahara
Mayakan Boko Haram sun kashe sojoji uku da wasu fararen hula takwas tare da raunata wasu da dama a garin Monguno da ke jihar Borno, bayan sun kutsa cikin dakarun sojojin da wata mota mai dauke da bamabamai.
Wannan harin na zuwa ne bayan kwanaki 10 da janye sojojin Chadi da ke taimakawa takwarorinsu wajen yakar Wani bangare na ‘yan kungiyar Boko Haram ISWAP da ke yankin tafkin Chadi a Areawacin jihar Borno.
A wani rahoton da sojojin suka fitar na cewa, a jiya Alhamis an yi musayar wuta tsakanin Sojojin da ‘yan Boko Haram a shataletalen Monguno.