’Yan Boko Haram sun kone babban masallacin Izala a harin Damaturu

’Yan Boko Haram sun kone babban masallacin Juma’a na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah a harin da suka sake kai wa Damaturu a karshen makon jiya. Harin ya haddasa konewar masallacin Jumu’ar da shaguna sama da 20 tare da salwantar dukiya ta miliyoyin Naira, kamar yadda Aminiya ta gano.Maharan sun kai harin ne […]

’Yan Boko Haram sun kone babban masallacin Izala a harin Damaturu
’Yan Boko Haram sun kone babban masallacin Izala a harin Damaturu

’Yan Boko Haram sun kone babban masallacin Juma’a na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah a harin da suka sake kai wa Damaturu a karshen makon jiya.

Harin ya haddasa konewar masallacin Jumu’ar da shaguna sama da 20 tare da salwantar dukiya ta miliyoyin Naira, kamar yadda Aminiya ta gano.
Maharan sun kai harin ne da misalin karfe 6:00 a ranar Jumu’a, daidai lokacin da al’ummar birnin ke zaman dar-dar sakamakon harin da jami’an tsaro na JTF da hadin gwiwar ’yan banga suka kai maboyar ’yan kungiyar a garin Gujba inda suka kashe da damansu kamar yadda wata majiya ta shaida wa Aminiya.
Harin da ’yan bindigar suka kai Damaturu an dauki fiye da da awa biyar ana gumurzu tsakaninsu da jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda da ’yan baka, inda aka rika jin rugugin makaman atilare da tankokin yaki da bama-baman da aka rika amfani da su.
Maharan sun kone babban masallacin Jumu’a na farko na kungiyar Izala da manyan ofisoshin ’yan sanda biyu da wurin shakatawar manyan jami’an ’yan sanda na jihar da shaguna sama da 20 da gidajen jama’a.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, maharan wadanda suka rika kabbara suna jefa bama-bamai kuma sun rika cewa daga yanzu babu sassauci a tsakaninsu da jami’an tsaro da masu dukiyar garin. Malamin ya ce yana kyautata zaton jin karar tankar yaki ne ya tilasta maharan saurin janyewa daga yankin nasu.
A wani labarin kuma wasu ’yan kunar bakin wake biyu mata da wani namiji sun kai hare-hare a garin Potiskum inda suka hallaka mutum takwas ciki har ’yan sanda biyu da maharan da kuma wasu mutum uku.
Wata majiya a Potiskum ta shaida wa Aminiya cewa dan kunar bakin wake na farko bam din da ke cikin motarsa ne ya fashe lokacin da aka tsare shi domin bincike a ofshin ’yan sandan, inda ’yan sanda biyu suka rasu wasu suka jikkata, kuma wata majiya a ofishin ’yan sandan ta ce maharin ya tsere.
Su kuwa ’yan mata biyu masu matsakaicin shekaru sun kai hari ne a kusa da gidan daukar hoto na Photo Palace da ke kusa da kasuwar wayoyin hannu a ranar Lahadi da kasuwar Potiskum ke ci, inda suka tada bama-baman da ke jikinsu suka hallaka kansu da wasu mutum uku.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Yobe Mista Markus danladi ya tabbatar da faruwar hare-haren na Damaturu da Potiskum da kuma barnar da suka yi.