…’Yan Boko Haram sun kone barikin soja a Gombe
A ranar Asabar da ta gabata tun misalin karfe 6:00 na safe ’yan kungiyar Boko Haram suka shiga garin Gombe inda suka yi ta ba-ta-kashi da soja inda daga bisani suka kori sojojin suka kone barikinsu. Maharan sun shiga Gombe ne ta garin Dadin-Kowa mai nisan kilomita 44 daga Gombe suka bi ta Kwadom suka […]
A ranar Asabar da ta gabata tun misalin karfe 6:00 na safe ’yan kungiyar Boko Haram suka shiga garin Gombe inda suka yi ta ba-ta-kashi da soja inda daga bisani suka kori sojojin suka kone barikinsu.
Maharan sun shiga Gombe ne ta garin Dadin-Kowa mai nisan kilomita 44 daga Gombe suka bi ta Kwadom suka shiga Gombe ba tare da wata turjiya daga jami’an tsaro ba, inda suka rika raba wasu takardu daga Dadin-Kowa suna ce wa jama’a ba ruwansu da su amma kada su yarda a yi zabe kuma kada su fito a ranar zabe.
A takardar sun gargadi jama’a cewa duk wanda yake son ya yi nisan kwana to ya guje wa rumfunar zabe a ranakun zabe domin za su kai hare-hare kan rumfunan.
Wannan hari na ’yan Boko Haram wanda suka shafe awa hudu suna yi, shi ne irinsa na biyu a Gombe, kuma a kan hanyarsu ta shiga Gombe sun kone wata motar daukar marasa lafiya a asibitin garin Hinna da ofishin ’yan sandan garin Kwadom kafin su kone barikin sojojin da ke fadar jihar.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Gombe DSP Fwaje Atajiri, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa har zuwa lokacin ba a tantance adadin wadanda suka mutu ko aka raunata ba.
Harin ya jawo kafa dokar hana fita na tsawon kwana biyu ba dare ba rana, inda a ranar Litinin, aka sassauta ta zuwa karfe 6:00 na safe zuwa 8:00 na dare.