’Yan Boko Haram sun kwace garin Marte a Borno

Rahotannin na bayyana cewa, ‘yan Boko Haram, a jiya Lahadi sun kwace hedkwatar karamar hukumar Marte da ke jihar Borno. Majiyarmu daga Maiduguri ta samu rahoton cewa, ‘yan Boko Haram din sun kai hari barikin sojoji na bataliya ta 153 da ke garin Marte, inda suka yi ta harbe-harbe  akan duk wanda suka samu tare […]

’Yan Boko Haram sun kwace garin Marte a Borno

Tsohon hoto.

Rahotannin na bayyana cewa, ‘yan Boko Haram, a jiya Lahadi sun kwace hedkwatar karamar hukumar Marte da ke jihar Borno.

Majiyarmu daga Maiduguri ta samu rahoton cewa, ‘yan Boko Haram din sun kai hari barikin sojoji na bataliya ta 153 da ke garin Marte, inda suka yi ta harbe-harbe  akan duk wanda suka samu tare da kone gidajen jama’ar garin.

Rahotan ya kara da cewa, ‘Yan Boko Haram sun ce, sun shiga garin ne ba da niyyar kashe kowa ba sai dai kawai su kwace garin. Sun kaiwa sojojin harin ne da misalin karfe 6 na yamma gab da shan ruwa.