’Yan Boko Haram sun sako mata da yara 192 a Yobe
Kimanin mutum 192 wadanda akasarinsu mata da yara ne suka samu kansu bayan ’yan Boko Haram da suka yi awon gaba da su a harin da suka kai kauyen Katarko da ke karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe suka sako su. Wata majiya ta kusa da mutanen da Boko Haram suka sako ta shaida wa […]
Kimanin mutum 192 wadanda akasarinsu mata da yara ne suka samu kansu bayan ’yan Boko Haram da suka yi awon gaba da su a harin da suka kai kauyen Katarko da ke karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe suka sako su.
Wata majiya ta kusa da mutanen da Boko Haram suka sako ta shaida wa Aminiya cewa, ’yan Boko Haram ne da kansu suka sake su ta hanyar tantance mutanen da suka yi garkuwa da su daga cikin su 218 daga kauyen Katarko a harin da suka kai kimanin mako hudu da suka shude.
Wani magidanci da ya samu iyalansu uku daga cikin hudu da ’yan Boko Haram suka tsere da su a harin da ya nemi da a boye sunansa ya ce an sanar da shi cewa an yi waya ga wani kansilansu cewa ga mutanen Katarko nan da aka gudu da su ’yan kungiyar sun sako su sun ajiye su a kauyen Wuro Yunwa, don haka a je a debo su. Ya ce nan da nan labarin ya bazu a garin Damaturu, inda jami’an karamar Hukumar Gujba suka tura motoci don dauko su, inda aka same su a kauyen Ngirbuwa wurin da ’yan kungiyar suka kai su daga baya.
Ya kara da cewa, bayan da ya samu labarin an kawo mutanen Damaturu ne ya tafi wurin da aka ajiye su sai ya tarar da uku daga cikin iyalansa saura guda kuma an ce nan gaba kadan ana iya sako su.
daya daga cikin matan da suka samu kansu mai suna Ya-Kellu mai kimanin shekara 60 da ta ki a dauki hotonta ta shaida wa Aminiya cewa, ’yan kungiyar ne suka tara su wuri guda inda suka umarce su cewa, duk wanda ke son zama da su ya koma gefen Kudu wadanda kuma ba su son ci gaba da zama da su, to su koma gefen Arewa daga baya sai suka ce su wadanda ba su son zama da su su tafi an sallame su, tunda sun zabi komawa kasar dagutu don haka su ma sun zama dagutu, shi ne suka debo su zuwa kauyen Ngirbuwa.
Ta ce, lokacin da ’yan bindigar suka rabo su da kauyensu Katarko ba su bar su wuri guda ba sun rarraba su ne wuri-wuri inda suka kai wasu garin Buni Yadi wasu kauyen Ajigin kuma babu abin da suke ci sai wake da gishiri, yayin da kullum mata ke sussukar wake da
dawa da gero da sauran ayyuka na wahala kamar bayi.
Ta ce, babban abin bakin ciki shi ne ’yan bindigar sun kwace ’ya’yansu maza da sunan wai za su sanya su a makaranta.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin Shugaban karamar Hukumar Gujba kan lamarin ko wani jami’in tsaro hakarta ba ta cimma ruwa ba.