’Yan Boko Haram sun tarwatsa gadar da ta hada Najeriya da Kamaru
’Ya’yan kungiyar Boko Haram sun tarwatsa wata babbar gada da Ngala a Jihar Borno da ta hade kasashen Najeriya da Jamhuriyyar Kamaru.Tarwatsa gadar ya haddasa katse daya daga cikin muhimman hanyoyin sufuri a tsakanin Najeriyar da Kamaru abin da zai iya jawo tsaiko wajen kai wa mutane kayayyakin agaji.Mazauna yankin sun ce akwai tarin kananan […]
’Ya’yan kungiyar Boko Haram sun tarwatsa wata babbar gada da Ngala a Jihar Borno da ta hade kasashen Najeriya da Jamhuriyyar Kamaru.
Tarwatsa gadar ya haddasa katse daya daga cikin muhimman hanyoyin sufuri a tsakanin Najeriyar da Kamaru abin da zai iya jawo tsaiko wajen kai wa mutane kayayyakin agaji.
Mazauna yankin sun ce akwai tarin kananan da manyan motoci dauke da kayan masarufi da suka kasa tsallakawa ta gadar Ngala.
Garin na Ngala na kan iyakar Najeriya da Kamaru inda dubban mutane daga kasashen biyu ke gudanar da harkokin kasuwanci.
Hakan na zuwa ne a yayin da Hafsan Hafsoshin Sojan Najeriya, Laftanar Janar Kenneth Minimah ya ce wasu sojoji sun arce daga bakin aikinsu saboda tsoron Boko Haram.
Janar Minimah ya ce lamarin abin Allah wadai ne kuma ya nuna cewa mutanen ba su dace da shiga aikin soja ba.
Ya kara da cewa sojan asali ba zai guje wa yaki ba, saboda an dauke shi aiki ne domin ya kare martabar kasarsa kuma ya je fagen daga.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin hukumomin Najeriya da kin lura da sojojin da ke yaki da Boko Haram ko ba su hakkokinsu yadda ya kamata.
Bayanai sun nuna cewa dakarun da ke yaki da ’yan Boko Haram a Jihar Borno ba su da cikakkun kayan aiki, abin da ya sa suke fuskantar asarar rayuka.
Kuma a wannan mako wai jirgin sojan sama mai saukar ungulu ya fado a Jihar Borno inji hukumomin soja, yayin da wasu ke cewa ’yan Boko Haram ne suka harbor shi.
A watannin baya, wasu sojoji sun yi bore a Maiduguri inda suka harbi motar kwamandansu bisa zargin cewa ya sa’yan Boko Haram sun hallaka abokan aikinsu a wani kwanton bauna da suka yi musu. Sojoji 18 yanzu haka suna fuskantar tuhumar a kotun soja kan wannan bore.